Chelsea ta yi nasarar lashe Champions League na bana, bayan da ta doke Manchester City da ci 1-0 ranar Asabar a Porto, Portugal.
Kai Havertz ne ya ci kwallon da ya bai wa Chelsea kofin Zakarun Turai karo na biyu a tarihi.
Wannan shi ne karon farko da kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya lashe Champions League a tarihin sana'ar horar da tamauala.
Ko a bara sai da ya kai Paris St Germain wasan karshe, amma Bayern Munich ta yi nasara da ci 1-0.
Cikin watan Janairu Paris St Germain ta sallami Tuchel, wanda Chelsea ta dauka ya kuma maye gurbin Frank Lampard a lokacin da kungiyar ta fita daga hudun farko.
Chelsea ta karkare kakar Premier ta bana a mataki na hudu duk da rashin nasara da ta yi a gidan Aston Villa a wasan karshe, yayin da Liverpool ce ta kammala a mataki na uku.
Wannan shi ne karon farko da City wadda ta lashe kofin Premier League ta kai wasan karshe a Champions League.
Pep Guardiola wanda yake da Champions League biyu da ya lashe a Barcelona ya fara karawar da Fernandinho da kuma Rodri a benci, inda ya jere masu cin kwallaye a gaba.
City ta samu damar makin zura kwallao a raga tun kan hutu, har da wadda Phil Foden ya buga amma Antonio Rudiger ya hana kwallon shiga raga.