Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta yi zargin cewa saboda gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC ne kamfanin sada zumunta da muhawara na Twitter ya zabi kasar Ghana domin kafa reshensa na Afrika, maimakon Najeriya.
A cewar PDP babu wanda zai zo ya zuba jari a Najeriya, ganin yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kassara abubuwa da dama, kama daga kan tsaro da rashin wutar lantarki da kuma cin-hanci da rashawa da ya ƙaru.
PDP ta ce babu inda ya kamata kamfanin ya bude reshensa face Najeriya, domin duk Afrika babu kasar da ke da yawan masu amfani da shafin kamar Najeriya, amma saboda gazawar gwamnatin APC wajen samar da tsaro da wuta, sai ya zabi Ghana, ya tsallake Najeriya.
Sanata Umar Ibrahim Tsauri shi ne sakataren jam'aiyyar na kasa, ya kuma bayyana wa BBC cewa: ''Babu wani tsari da ke aiki a Najeriya, ba wutar lantarki, babu tsaro, tsarinmu na tattalin arziki ba ya aiki a karkashin wannan gwamnatin'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa hatta matsalar cin-hanci da rashawa da ta ƙaru a wannan gwamnati na rage wa masu zuba jari da 'yan kasuwar kasashen waje kwarin guiwar zuwa kasar domin sanya hannun jari da kuma bude harkokin kasuwanci.
'Yan Najeriya da dama dai sun yi imani da cewa shawarar da kamfanin Twitter ya yanke ta zama butulci ga kasar da ke a matsayin mafi karfin tattalin arziki a nahiyar, wadda ke taimaka wa kamfanin fiye da kowacce kasa a Afrika.
Wani binciken NOI, ya gano cewa 'yan Najeriya miliyan 39.6 na da shafin Twitter, adadin da ya zarce yawan al'ummar Ghana baki daya.
A cikin sanarwar da ya fitar ta yanke hukuncin, Twitter ya bayyana Ghana "a matsayin kasar da ta ciri tuta ta fuskar kare dumokuradiyya, kuma mai goyon bayan 'yancin fadin albarkacin baki''.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya ce, "zabar kasar ta Ghana a matsayin hedikwata ga ayyukan Twitter a Afirka labari ne mai matukar kyau'' inda ya bayyana alakar a matsayin kyakkyawan kawance tsakanin Ghana da Twitter.