Menu

Twitter zai fara matsa muku sauya tunani kafin ku tura kalaman zagi a shafin

 118408510 6ee025c2 7114 4073 A554 533fb51c506b Ka sauya tunani kafin ka tura kalaman zagi, inji Tuwita

Fri, 7 May 2021 Source: BBC

Daga yanzu shafin Twitter zai dinga matsa wa mutane su sake duba "kalaman zagi ko waɗanda da ba su dace ba" kafin su wallafa su a dandalin.

Dandalin sadarwar wanda ya sha fuskantar suka kan kalaman rashin kyautawa, ya fara gwada tsarin a shekarar da ta gabata.

Twitter ya ce sakamakon gwajin ya nuna raguwa a yawan kalaman zagi a dandalin.

A ranar Laraba ne kamfanin ya ce zai bai wa masu amfani da turancin Ingilishi damar fara amfani da shirin a kan wayoyin Apple da Android.

Twitter ya ce sun gano matsawar ta sa kashi 34 cikin 100 na mutune sun sauya saƙon da suka yi niyyar wallafawa ko kuma sun fasa turawa gaba ɗaya.

A cewarsa, masu amfani da shafin sun rage wallafa zage-zage ko cin zarafi da kashi 11 cikin 100 bayan an matsa musu a karon farko.

Kazalika, su ma ba lallai ne a zage su ba ko kuma yi musu kalaman ɓatanci.

Da ma shafin na amfani da shigen wannan shiri domin rage yaɗa labaran ƙarya, inda ake matsa wa mutum ya shiga adireshin wani labari da yake son yaɗawa ya karanta kafin ya sake yaɗa shi.

Source: BBC