Menu

Umrah: Yadda cutar korona ta sauya yadda ake ɗawafi

 118332859 2f30c084 0f1f 48a0 9e36 508762779972 Ɗawafi na ɗaya daga cikin ayyukan ibada a lokacin aikin Hajji da Umra

Wed, 5 May 2021 Source: BBC

Ɗawafi na ɗaya daga cikin ayyukan ibada a lokacin aikin Hajji da Umra da masu ibada ke taruwa har a yi ta turmutsutsu wajen gudanar da shi.

Sau da yawa wasu kan samu rauni ko su rasa rayukansu ma a lokacin yin ɗawafi musamman lokutan Hajji da Umra saboda cunkoso na mutane masu kewaye ɗakin Ka'aba.

Babu mamaki, a shekarun baya da za a ce akwai lokacin da zai zo da ba za a riƙa cunkoso a lokacin ɗawafi ba, ba lallai ku yarda ba.

Amma ɓullar cutar korona a faɗin duniya ta sa dole aka sauya yadda ake gudanar da abubuwa da dama na yau da kullum ciki kuwa har da ayyukan ibada - kamar sallah cikin jam'i da daidaita sahu a sallar da ma yadda ake ayyukan Hajji da Umra kamar shi ɗawafin da safa da marwa da dai sauransu.

Da yake ɗawafi na ɗaya daga cikin manyan ayyukan Umrah da Hajji, hukumomin Saudiyya sun samar da hanyoyin yin sa yadda ba za a saɓa dokokin cutar korona ba.

A yanzu an sanya alama a ƙasan filin ɗawafi don nuna wa masu ɗawafi yawan tazarar da ya kamata su bari a tsakaninsu.

Kamar yadda aka saba dama, akwai ƴan sanda ko jami'an masallaci da ke shawagi a filin ɗawafi tun kafin zuwan cutar korona amma a masallacin Ka'aba yanzu, akwai jami'an masallaci na musamman da ke sa ido domin tabbatar da cewa maniyyata sun bar tazarar da ya kamata wato ba su cunkushe a wuri guda kamar yadda aka sani ba.

Dama kuma akwai iya adadin mutane da ake bari su shiga masallacin a lokaci guda ta hanyar amfani da wata manhaja don haka zai yi wuya a samu cunkoson mutane.

Sannan duk da tazarar da ake bari, dole ne mai yin ɗawafi ya sanya takunkumin fuska har ya fita daga masallaci.

Haka kuma, ba kamar yadda aka saba ba yanzu masu sanye da Ihrami ne kawai ake bari su shiga filin ɗawafi, amma su ma ba a bari su je kusa da Ka'aba.

An kewaye Ka'abar da wasu robobi da za su hana mutane wucewa su je kusa da ita.

Don haka babu taɓa Ka'aba da Hajrul Aswad da tsayuwa a ƙarƙashin indararon rahama kamar yadda aka saba.

Akwai wasu ma'aikata na musamman a masallacin wanda aikinsu shi ne tsaftacce filin ɗawafi da wasu na'urori masu fitar da sinadaran tsaftace iska da nufin kashe ƙwayoyin cutar korona.

A baya babu irin wannan duk da cewa akwai masu sharar masallaci da ke aiki ba dare ba rana wajen sharewa da goge ƙasan filin.

Cutar korona ta kawo sauye-sauye da dama a yadda ake gudanar da ayyukan ibada kama daga yin sallah a jam'i zuwa ayyukan Umrah kamar shi ɗawafin da Safa da Marwa da dai sauransu.

Hatta da shiga ƙasar ta Saudiyya a yanzu tsare-tsaren sun sauya sosai kuma an ƙaddamar da sabin hanyoyin shiga don yin ayyukan ibada.

Ana sa rai za a samu sassauci musamman tunda yanzu an samar da allurar rigakafin cutar kuma hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa wanda duk ya yi allurar yana iya shiga ƙasar don yin ibada.

Akwai fatan cewa nan da shekaru masu zuwa, ana iya komawa gudanar da ayyukan ibada kamar yadda aka saba kafin ɓullar cutar.

Source: BBC