Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sandan kasar.
Sabon sufeton zai maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.
Ministan harkokin 'yan sanda Maigari Dingyadi ya bayar da sanarwar ranar Talata.
Ranar 4 ga watan Fabrairu ne Shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin Mohammed Adamu da wata uku kodayake wata biyu kawai ya yi .
Tarihin Usman Alkali Baba
An haifi DIG Usman Alkali Baba a garin Geidam na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar 1 ga watan Maris na 1963.
Ya kammala Digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano a 1985.
Kazalika ya yi Digiri na biyu a Jami'ar Maiduguri a kan Harkokin Mulki a 1997.
Ya shiga aikin dan sanda a 1988 kuma ya rike manyan mukamai a bangarori daban-daban.
Mukaman da ya rike sun hada da mataimakin babban sufeton 'yan sandan a kan harkokin kudi da mulki, mataimakin babban sufeton 'yan sandan a gunduma ta 5 da ke Benin, da gunduma ta 4 da ke Makurdi, da gunduma ta 7 da ke Abuja.
Haka kuma DIG Baba ya taba rike Kwamishinan 'yan sanda na Abuja da jihar Delta.
Kafinnadin nasa a matsayin sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, ya shugabanci sashen binciken masu aikata manyan laifuka wato Force Criminal Intelligence and Investigation Department (FCIID).
DIG Alkali mamba ne a Kwalejin Tsaro ta Kasa da kuma kungiyar manyan jami'an 'yan sanda ta duniya.
Yana da mata da 'ya'ya.