Menu

Wannan ce kaka mafi muni da nake fuskanta — Klopp

 117496120 Gettyimages 1137416764 Kocin Liverpool Jurgen Klopp

Tue, 9 Mar 2021 Source: BBC

Jurgen Klopp ya ce wannan ce kaka mafi muni da yake fuskanta a shekara 20 da yake horar da tamaula, bayan da Liverpool ta sha kashi karo shida a jere a gida.

Ranar Lahadi, Fulham ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a gasar Premier, kuma wasa na shida a jere da aka doke kungiyar a gida.

A bara ne Liverpool ta lashe Premier League da tazarar maki 18 da yin wasa 68 ba tare da an doke ta ba a Anfield.

Sai dai kakar bana ta sa Liverpool cikin kalubale, bayan wasa 28 ta hada maki 43 tana ta takwas a teburin Premier League.

Kungiyar ta yi rashin nasara a karawa shida daga wasa bakwai da ta buga a baya, hakan zai iya shafar kwazon kungiyar a Champions League.

Kocin dan kasar Jamus, mai shekara 53 ya ja ragamar Borussia Dortmund da ta lashe Bundesliga biyu a jere a kakar 2010-11 da kuma 2011-12.

Sai dai Dortmund ta karkare kakar 2012-13 a mataki na biyu da tazarar maki 25 tsakaninta da Bayern Munich wadda ta lashe kofin a kakar.

Klopp ya bar aikin horar da Dortmund a 2014-15, bayan da kungiyar ta karkare gasar Bundesliga a mataki na bakwai a teburin.

An bai wa Klopp aikin jan ragamar Liverpool a shekarar 2015.

Ya kuma kai kungiyar wasan karshe a Champions League a 2018, inda Real Madrid ta lashe kofin.

Sai dai a kakar 2019 Liverpool ta ci Champions League, bayan da ta yi nasara a kan Tottenham.

A kakar 2019-20, Liverpool ta lashe Premier League, bayan karawar mako na 31 ta kafa tarihin cin kofin saura fafatawa bakwai a karkare gasar a tarihi.

Ta kuma yi kan-kan-kan wajen hada maki 55 a gida da cin karawa 18 da canjaras daya.

Doke Liverpool wasa shida a jere a gida a bana, shi ne mafi muna a tarihin gasar tun bayan wanda kungiyar ta Anfield ta yi a 1953-54 a lokacin ta yi ta karshe a teburi.

Liverpool ita ce ta farko da ta yi rashin nasara a wasa shida a jere a Premier League a gida, tun bayan Huddersfield Town a Fabrairun 2019.

Source: BBC