Menu

Wasika daga Afirka: Sarauniyar masarautar Efik tana son kawo sauyi a Najeriya

 117757323 Instal1 Sarauniyar Obong-Anwan

Mon, 12 Apr 2021 Source: BBC

Daga jerin wasikunmu na Afirka, a wannan makon 'yar jarida, marubuciya kuma 'yar Najeriya Adaobi Tricia Nwaubani ta mana duba kan rawar da sarakunan gargajiya suka taka a karni na 21.

Saboda rashin tabbas daga 'yan siyasar Najeriya, Barbara Etim James ta amince cewa warwarewar matsalolin da kasar ke ciki sun dogara ne a kan yawancin sarakunan gargajiya da sarauniyoyi da kuma manyan mutane.

Shekaru biyu da suka wuce aka nada Etim mai shekara 54 sarauniyar masarautar Efik da ke kudancin Najeriya.

Duk da shafe shekaru 20 da ta yi a Birtaniya, da samar da asusun daidaito mai zaman kansa, ta ce ba ta da niyyar sauya tsarin mulkin shugabannin Afirka da maye gurbinsu da na zamani.

"Tsarin zamani na nufin sauya abin da aka gada," in ji ta.

Ms James na son kawo wani tsarin.

"Ina son kawo tsarin ci gaban al'ada, daga abin da na koyo ba wai na mayar da al'adar ta zama ta zamani ba."

Ms James tana gwamutsa matsayinta na sarauniya da shugabar asusunta, da yawan tafiye-tafiye daga jiharta ta Calabar, zuwa biranen Lagos da Abuja domin gudanar da aiki.

"Calabar gida ne, amma na fi zama a wasu jihohin. Amma akwai ayyukan da nake yi a nan."

Ana bukatar masu rike da mukaman gargajiya su dinga zuwa fada a duk wata, domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi al'umma, don haka duk wata take zuwa gida daga duk inda take, tsarin da take fatan fasahar zamani za ta sauya.

"Ina tattaunawa da su kan yin taronmu ta internet," in ji ta.

Da fari matakin ka iya zama bambarakwai ga wasu mutanen ko ma wasu su yi masa kallon raini ne a gayyato sarakunan gargajiya ta hanyar aikewa da sakon waya ko kira, ko aika musu katin gayyata ta intanet, in ji Ms James.

"Amma ai suna farin ciki idan aka tura musu kudi ta asusun ajiya na banki, ta amfani da wayar salula."

Batun da take amfani da shi ke nan wajen kafa hujjarta na komawa amfani da fasaha a duk lokacin da ake tattaunawa kan batun.

'Yan siyasar wucin gadi

Kundin tsarin mulki Najeriya bai bayyana mukaman sarakunan gargajiya ba, wasu na ganinsu a matsayin wadanda ba sa taka rawar da ta dace.

Batutuwan tsige su daga mukami saboda rashin bai wa 'yan siyasa goyon baya, sun sake bayyana yadda ba a dauke su da ƙima ba, tare da ɗiga ayar tambaya kan karfin ikon da suke da shi.

Ba su da takamaimai kudaden shiga na kashin kansu. Amma Miss James ta amince mutane irin ta za su iya kawo sauyi fiye ma da 'yan siyasa.

Ta bukaci sarakunan gargajiya su yi kokarin zama makusantan jama'a fiye da zaɓaɓɓun 'yan siyasa, ta hanyar bayanan da suke samu za su fi sanin abin da ke faruwa a cikin al'umma.

Hakan na nufin za su fi yi wa mutane amfani fiye da 'yan siyasa, musamman wajen batutuwan tsaro da talauci musamman kasancewarsu akan mukami na dogon lokaci, in ji James.

"Gwamnonin jihohi na kwashe shekarar aiki ta farko wajen daidaita zamansu, shekara ta biyu su fara ayyuka, shekara ta uku shirye-shiryen zabe, shekara ta hudu ana zabe," in ji Miss James.

"Ba su da wa'adin mulki mai tsawo, zuwa suke suna tafiya, amma sarakunan gargajiya kan zauna a kan karaga har karshen rayuwarsu."

Duk da cewa akwai kudaden da ake warewa kananan hukumomi, daidaikun sarakunan gargajiya ne ake sanyawa cikin manufofin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummarsu.

"Muna da manyan 'yan boko, amma ba sa tunanin abin da zai kawo wa tattalin arzikinmu ci gaba."

"Kawai abin da ake yi shi ne ɗiba ake yi ba a bunkasawa. Ayi ta bukukuwa, taruka, babu tunanin abin da za a hada karfi da karfe wajen aiwatarwa? Ta yaya za ka mallaki kasuwancin kanka? Za ka iya mallakar gona? Duk babu."

Ta kafa gidauniyarta, da take bai wa sabbin 'yan kasuwa bashi.

Da wadanda ke son fadada kasuwancinsu, tana shirya tarukan da za a koya wa mutane yadda za su yi kasuwanci ko wata sana'a.

Ta ce tana son mutane su dinga tunanin yadda za su samu kudi da yadda za su kashe su ta hanyar da ta dace.

Uba abin koyi

Sarki Obong shi ke jagorantar masarautar Efik, wadda ke garin Calabar na gabar teku da ke jihar Cross River, masarautar na kunshe da gidajen sarauta da garuruwansu ciki har da garin Henshaw.

A shekarar 2019 aka nada ta sarauniyar Abog-Anwa ta garin Henshaw, saboda gudummawar da take bai wa masarautar. Mahaifiyarta wadda a baya ita ce sarauniyar Obong-Anwan, ta rasu a shekarar 2016, sai dai sarautar ba ta gado ba ce.

Kowane gida zai iya samun sarauniya amma yawanci ba su da ita.

"Abu na farko nauyi ne ya hau wuyanka domin ka taimaka wa mutane. Akwai kashe kudi. Akwai abubuwa da dama tattare da mukamin," in ji Miss James, inda ta ce yawancin tarukan da take shiryawa daga lalitarta kudin ke fitowa, ko wasu mutanen da ta sani na daban.

Soyayyar da sarauniyar ke yi wa jama'arta ta samo asali tun tana 'yar karama, lokacin da take kwaikwayon abin da mahaifinta Emmanuel Etim James - yake yi wanda mataimakin kwamishinan 'yan sanda ne a wancan lokacin, daga bisani ya koma aiki da wani kamfanin hakar man fetur mai zaman kansa.

"Duk abin da ya samu a kasashen duniya, ya dawo da su gida. Yana shiga a dama da shi a kowane fanni.

Ya gina katon gida a garinmu, ya kuma taimaka wa mutane su gina gidajensu ta hanyar ba su kyautar siminiti, wannan da idona na gani," in ji ta.

Bayan kammala digiri a fannin na'ura mai kwakwalwa a Jami'ar Lagos, sai ta koma Birtaniya don yin digiri na biyu a fannin kasuwanci, ta kuma zauna a can.

Amma ba ta taba mantawa da tushenta ba.

"Yawan tafiye-tafiye da cudanya tsakanin al'umma, yana sanyawa ka mutunta inda kake.

"Abin sha'awa ne, abin burgewa.''

"Mutane da dama idan suka girma, suka waye sai su koma Lagos ko Abuja, ba sa mutunta ko daukar inda suka fito ko kauyukansu da muhimmanci. Amma na sha banban da irin wadannan mutanen."

'Mata gwaraza ne'

A shekarar 2009, suka rabu da mijinta don haka ta dawo Calabar. Sarauniyar Obong-Anwan ba lallai sai ta zama mai aure ba.

"Bisa al'adar Efik, matsayin mace ba ya alkanta ta da mijinta ko aure."

"Mu mata muna da karfin hali irin namu. "

Kusancin da ke tsakaninta da jama'arta da kan abin da ya wuce, bai sa sun juyawa alaka tsakaninsu da Turawan mulkin mallaka baya ba.

Efik ta kasance mai shiga tsakani a lokacin cinikin bayi, da tafinta tsakanin turawan Birtaniya da mutanen Calabar ta fuskar kasuwanci.

Yawancin mazauna yankin sunan Ingilishi suke amfani da shi, misali kamar Duke, Henshaw, James da sauransu. Har wa yau suturar da mata da maza ke sanyawa tun na zamanin mulkin sarauniya Victoria ne.

Mutanen sassan Najeriya sun so daina amfani da irin abubuwan da ke tuna musu da lokacin mulkin mallaka, ta hanyar sauya sunayen iyayensu ko tituna ko garuruwa, amma Miss James ta ce ba ta ga amfanin haka ba.

"Al'ummar Efik su na ganin babu bukatar wadannan sauye-sauyen.

"Ba wai saboda ba mu damu ko karanta abubuwan da suka faru a lokacin mulkin mallaka ba. Kawai muna ganin abin da ya faru ne kuma ba abin kunya ba," in ji ta.

"Abin da ya faru ya faru. Mun san abubuwa maras kyau da suka faru a lokacin mulkin mallaka da cinikin … kawai dai ba mu kullaci Turawan Birtaniya ba."

Maimakon haka, Miss James ta yi amanna da kamata ya yi kabilun Najeriya su mayar da hankali kan yadda za su kawo ci gaba da sauyin zamani da za su dorar da dabi'u da al'adunsu.

"Ta yaya za mu inganta makada da masu rawa na al'ada? Ta yaya za mu kubutar da harshenmu daga ɓata? Ta yaya za mu tabbatar al'adunmu ba su bace ba, mu kuma yarda su zuwa al'ummar da za ta zo nan gaba? "Abin da ta tambaya kenan.

Wadannan su ne abubuwan da take tattaunawa da jama'arta, batun da kuma ta ke son ganin ta ci gaba da yi a matsayinta na sarauniyar Obong-Anwan ta garin Henshaw da kuma shi ta ke so a dinga tunawa da ita.

Source: BBC