Wasu 'yan Najeriya sun fara bayyana adawarsu ga shirin gwamnatin ƙasar na kashe zunzurutun kuɗi har Dala Biliyan guda, domin gyara matatar man fetur mafi daɗewa a ƙasar ta Fatakwal, dake jihar Rivers.
Majalisar zartarwa ta ƙasa ce ta amince da fitar da waɗannan kuɗaɗe don yin gagarumin aikin a ranar Laraba.
Ita dai wannan matata ta shafe fiye da shekaru 50 tana aiki, kafin fara samun matsala a shekarun baya bayan nan, lamarin da ake ganin ya haifar da gagarumin cikar wajen tace man a cikin gida.
To sai dai yayin da gwamnatin ke cewa akwai buƙatar gyara matatar domin bunƙasa tace mai, wasu 'yan Najeriya na da ra'ayin cewa almubazzaranci ware kuɗi masu yawa irin wadannan don gyara matatar mai guda, kuma tsohuwa.
''Duk mai hankali ya san cewa duk abin da aka ce tsohon abu ne to gyaransa sai a hankali, na biyu matatar man nan wani kamfanin Japan ne ya yi, amma yanzu an ce 'yan Italiya ne za su yi wannan gyaran, anya za su iya kuwa ?, na uku an ce za a shafe fiye da watanni 44 ana gyaran, wannan ma wani abu ne dake tayar mana da hankali'' inji Abubakar Idris, wani ɗan Najeriya da ya bayyanawa BBC ra'ayinsa.
Ya kuma ƙara da nuna damuwa a kan makudan kuɗaɗen da aka ware don yin aikin, wanda a ganinsa da za a yi amfani da su wajen samar da wasu matatun man za a iya samar da ƙanana da yawa.