Menu

Watakila Serge Gnabry ba zai buga karawa da PSG ba

 117862764 Gnabryandsane Gnabry (hagu) tare da Leroy Sane

Tue, 6 Apr 2021 Source: BBC

Watakila Bayern Munich ta buga wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League da Paris St Germain ba tare da Serge Gnabry ba ranar Laraba.

Bayern wadda take ta daya a teburin gasar Bundesliga da tazarar maki bakwai na fama da 'yan wasan da ke jinya da suka hada da Robert Lewandowski da kuma Marc Roca.

Idan har Gnabry ba zai buga fafatawar ta ranar Laraba ba, watakila Leroy Sane ya maye gurbinsa.

Ita ma PSG za ta yi wasan na hamayya ba tare da 'yan kwallo da suka hada da Alessandro Florenzi da kuma Marco Verratti wadanda suka kamu da cutar korona a makon jiya.

Dan wasan Brazil, Neymar da Kylian Mbappe ne za su ja ragamar PSG a matakin masu zura kwallo a raga ranar Laraba a wasan da za a yi a Allianz Arena a Jamus.

A karshen mako ne Lille ta doke PSG a gida a gasar Ligue 1, a kuma karawar aka bai wa Neymar jan kati.

Karo na 10 kenan da PSG ta yi rashin nasara a dukkan fafatawa a bana, kuma koci Mauricio Pochettino na sa ran kawo karshen wasa 19 da Bayern ta yi a Champions League ba tare da an doke ta ba.

Kungiyoyin sun hadu a wasan karshe a kakar 2020 a Lisborn, inda Bayern Munich ta yi nasara da ci 1-0 ta kuma lashe Champions League na shida a tarihi.

Source: BBC