Bayanai sun tabbatar da cewa mazauna Geidam da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da tserewa daga garin sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a yankin.
Mazauna garin na Geidam wadanda BBC Hausa ta yi magana da su sun ce daruruwan mutane ne suke ci gaba da ficewa daga garin zuwa makwabtan garuruwa wasunsu ma a kafa domin kauce hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram.
Wani mutum da ya je kwaso kayansa a cikin garin domin ya tsere ya shaida mana cewa "an fara harbe-harbe ina cikin gida ina diban kayana. Abin da na debo kawai na fito na yi maza na bar garin. Su 'yan Boko Haram da sojoji suna gabas da gari suna ta harbe-harbe."
Ya kara da cewa mayakan na Boko Haram suna wata kasuwa kodayake mutane suna iya shiga garin su debi kayansu domin su fice daga Geidam.
"Sai [matar] ta shiga daki suka zauna da 'ya'yan surukarta su biyar da budurwa har an kai mata sadaki. Wannan jefa atilarin aka ce da aka yi na farkon nan wallahi ba a sani ba, Allah shi ya bar wa kansa sani kawai aka ji karar abu. Sai surukar ta fito tana salati daki ya kama da wuta," in ji ta.
Ta kara da cewa yanzu ita ce ta ke shayar da ɗiyar 'yar uwarta da harin na atilari ya kashe.
Matar ta ce yanzu sun fice daga garin na Geidam tana mai cewa "mun fito a kafa mu da 'ya'ya muna kuka kamar dabbobi."
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce suna cikin tsaka mai-wuya sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram da suka tayar musu hankali tun ranar Juma'ar makon jiya.
Mai Mala ya ce sanin kowa ne halin da ake ciki a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sai dai hare-haren da suke gani a yanzu na tada hankula matuka kuma ya zama dole a tunkare su.
A tattaunawarsa da BBC, gwamna ya ce a baya komai ya yi sauki amma a wannan lokaci abin ya tsananta, saboda ba a san dalilan mayakan ba, kuma zuwansu na wannan lokaci ya sha bamban da wanda aka saba gani a baya.
A nata bangaren, rundunar sojin kasar ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 21 a garin na Geidam.
Kakakin rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima ya ce suna fuskantar kalubale wajen fitar da 'yan Boko Haram daga garin saboda sun saje cikin jama'a.