Sama da ƙungiyoyi 100 a Ingila suka yi ƙoƙarin lashe kofi huɗu a kaka ɗaya amma suka kasa tsawon shekaru.
Manchester City na cikin ƙungiyoyin Ingila da suka yunƙuro amma suka kasa kafa tarihin a baya - Ko Manchester City za ta zama ta farko da ta kafa tarihin? Shin kofi ɗaya ko biyu ko uku ko duka huɗun za ta lashe?
Babu wata ƙungiya da ta lashe kofin Premier da na zakarun Turai da na FA da kuma n Carabao ƙalubale a kaka ɗaya, amma wannan ne karo na huɗu da Man City ke yunƙurin lashe kofunan a shekaru bakwai.
Wataƙila saboda yau da gobe da kuma ƙwarewa wajen farautar manyan kofunan a makwannin ƙarshe na kaka zai iya yin tasiri a wannan karon ga Manchester City.
City za ta iya gyara matsalolin da ta fuskanta daga darussan da ta koya na kasa lashe kofunan a kaka ɗaya.
Ƙalubalen da ke gaban City
Wasannin da ke gaban Man City a harin lashe kofi huɗu a kakar 2020-21
| |||
---|---|---|---|
Competition
| Zagayen bab da na kusa da ƙarshe
| Zagayen dab da ƙarshe
| Zagayen ƙarshe
|
Carabao
| Tottenham
| ||
FA
| Chelsea
| Leicester/Southampton
| |
Zakarun Turai
| Borussia Dortmund
| Bayern Munich/PSG
| Real Madrid/Liverpool/Porto/Chelsea
|
A yanzu babban ƙalubalen da ake gani zai iya tarwatsa burin Manchester City shi ne haɗuwarta da Bayern Munich ko Paris St-Germain a zagayen kusa da ƙarshe idan har ta doke Borussia Dortmund a kwata fainal.
Lashe kofunan zai kasance babbar nasara da wata ƙungiya a Ingila ta samu a tsawon shekaru 133.
Sau biyu Pep Guardiola ke ƙaƙarin kafa tarihin a kaka biyu da suka gabata amma daga ƙarshe ya kasa.
A bana an sauya lokacin da aka saba buga wasan ƙarshe na lashe kofin Carabao daga watan Fabrairu.
City za ta fara bikin lashe kofin farko idan ta doke Tottenham a wasan ƙarshe na Carabao a Wembley da za su kece raini a ƙarshen Afrilu.
Ƙungiyoyin Ingila 15 da suka kusan lashe kofi huɗu da kaka ɗaya
| |||
---|---|---|---|
Matsayi/Ƙungiya
| Yunƙuri
| Shekarar da aka fi ƙwazo?
| Kawo ƙarshen buri?
|
1. Chelsea
| 15
| 2006-07
| 1 Mayu
|
2. Man Utd
| 23
| 2008-09
| 19 Afrilu
|
3. Man City*
| 11 | 2018-19
| 17 Afrilu
|
4. Burnley
| 1
| 1960-61
| 15 Maris
|
5. Arsenal
| 21
| 2010-11
| 27 Fabrairu
|
6. Nott'm Forest
| 3
| 1978-79
| 26 Fabrairu
|
7. Liverpool
| 23
| 1982-83
| 20 Fabrairu
|
8. Tottenham
| 5 | 2018-19
| 24 Janairu
|
9. Newcastle
| 3
| 1997-98
| 10 Disamba
|
10. Leeds
| 4
| 1974-75
| 13 Nuwamba
|
11. Aston Villa
| 2
| 1981-82
| 19 Janairu
|
12. Blackburn
| 1
| 1995-96
| 29 Nuwamba
|
13. Derby
| 2 | 1972-73
| 9 Oktoba
|
14. Leicester
| 1
| 2016-17
| 20 Satumba
|
15. Everton
| 1
| 2005-06
| 24 Agusta
|
*Ba a haɗa da kakar 2019-20 daka jinkirta ba
|