Menu

Yadda fasinjojin Algeria suka makale a Paris

 117627775 Cfe3013d Ad90 46bd B428 4fafa615c5a3 Yan Algeria 26 sun makale a filin jirgin a Paris

Fri, 19 Mar 2021 Source: BBC

Yan Algeria 26 da za su koma gida daga Birtaniya sun makale a filin jirgin saman Charles de Gaulle da ke birnin Paris makonni uku da suka gabata.

Fasinjojin wadanda suka hada da yara mata biyu da wata tsohuwa mai shekara 75 sun shigo Faransa ne a ranar 26 ga watan Fabareru daga filin jirgin sama na Heathrow.

Bayan isowarsa Paris kamfanin jirgin sama na Air Algeria ya fada mu su cewa ba za su ci gaba da tafiyarsu ba saboda matakan dakile bazuwar annobar korona.

Tun bayan wannan lokaci suna rayuwa cikin mawuyacin hali a mashigar Terminal 2 ta filin jirgin sama na Charles de Gaulle.

Ofishin jakadancin Algeria da ke Paris ya shaida wa BBC cewa kamfanin Air Algeria ya fada wa fasinjojin cewa an soke tikitinsu bayan da aka samu bular nau'in cutar korona na Birtaniya a kasar ta Algeria a ranar 25 ga watan Fabareru.

Tun bayan isowarsu filin jirgin sama suna barci ne a kan kujera ko kasa tare da cin abincin da mutane suka basu. Ana kuma yi wa daya daga cikinsu magani a wani asibiti.

Kamfanin Air Algeria na gwamnatin kasar ya rika basu abinci kyauta tun farko amma daga bisani ya dakatar da yin haka bayan da suka yi watsi da tayin da kamfanin ya yi mu su na mayar da su Birtaniya.

Source: BBC