Menu

'Yadda na kama mijina yana kallon hotunan batsa a intenet'

 117584352 Mediaitem117584351 An shawarci mutane su mayar da hankali kan saabuwa da kallon hotunan batsa

Thu, 18 Mar 2021 Source: BBC

An shawarci mutane su mayar da hankali wajen kula da alamomin da ke nuna wani daga cikin iyalansu na kallon hotunan batsa a shafukan intanet.

Gidauniyar 'Stop it Now' ta ce an samun ƙaruwar kiraye-kiraye a waya don neman taimako kan cin zarafi a Burtaniya da kashi kusan 50 cikin 100 a lokacin annobar cutar korona.

Gidauniyar ta ce zaman gidan da aka rinƙa yi a lokacin dokar kulle wataƙila ya taka rawa wajen bankaɗo irin wannan ɗabi'a a cikin gida.

Sarah - ba sunanta na asali ba ne - daga Wales ta bayar da labarinta da fatan ganin hakan ya taimaki sauran al'umma.

An cafke mijinta da suka shafe shekaru 25 tare shekarun kusan biyar da suka wuce bayan samunsa da hotunan batsa na yara.

"Na rasa tantance abin da yake yi har sai da ƴan sanda suka kai samame gidanmu a wata safiya ni kuma ina bene ina shirin fita aiki," a cewarta.

"Wataƙila ya gane girman laifin da ya aikata, amma ya ci gaba da shaida min cewa, 'shi ba mai lalata yara ba ne'."

Ƴan sanda sun dauke mijin nata domin yi masa tambayoyi da cire duk wata na'ura da kayan laturoni daga gidan.

Da yammaci a wannan ranar, Sarah ta samu damar magana da shi a ƙeɓe a ofishin ƴan sanda, a lokacin ne ya amsa cewa yana kallon hotunan ɓatsa na yara kusan shekara 10, ciki har da haramtattun hotuna a tsawon shekara biyu.

"Na kaɗu sosai da ɗimauta," a cewar Sarah.

"Bayan gano abin da mijina ya aikata, hakan ya kawo ƙarshen zamana da shi.

"Galibin mata na zaɓin ci gaba da rayuwa da abokan zamansu, amma ni na san auren mu ba zai ci gaba da kasancewa yadda yake ba."

Sarah ta shiga neman raba aurensu bayan ta fahimci cewa ba mutum ba ne da za ta sake yarda da shi.

Yanayin ya jefa ta cikin wani yanayi mara daɗi a matsayinta na malamar makaranta, yayin da take shirin sanar da ƴarta matashiya da ke karatu a jami'a wannan labarin.

"Akwai tsoratarwa yadda zan sanar da ɗiyata, kuma dole nayi hakan ta wayar tarho saboda dukkaninsu na karatu a ƙetare," a cewarta.

"Na shiga zulumi da fargaba, saboda idan ban yi gaggawa ba, watakila su tsinci labarin a shafukan sada zumunta.

"Ƴan sanda sun iso a motarsu sannan sun je ofishin mijina sun dauke kamfutarsa, don haka ba ni da masaniya kan abin da ake cewa tsakanin al'ummar yankinmu."

Dukkanin yarana mata sun yi ƙoƙari wajen sake dawo da alaƙarsu da mahaifinsu, sai dai Sarah, wacce tun wannan lokacin ba ta da aure, ta ce yanzu haka yana cikin "damuwa" da "rayuwar ƙasƙanci".

Ta ce yana da muhimmanci mutane su fahimci irin waɗannan alamomi.

Mijinta na da tarihi mai tsayi kan damuwa da rashin ƙwarin-gwiwa, yana fama a wajen aiki da yawan damuwar wataƙila wata rana a tilasta masa barin aikin.

Sarah ta shiga zargi da fahimtar cewa akwai abin da ke faruwa, don haka makonni kafin a cafke shi, ta kira shugabansa na wurin aiki domin bayyana damuwarta.

Ta yi tunanin cewa shafe dare da yake yi a kan kamfuta yana fama da rashin bacci wataƙila yana karance-karance ne a kan abubuwan da yake da sha'awa, kamar wasanni.

"Na so a ce na yi hikima a wannan lokaci ban kasance mai saurin yarda ba, da rashin ankara ba," a cewar Sarah.

"Yaran da aka ci zarafinsu su ne ainihin waɗanɗa aka yi wa laifi."

Ta ce yana da muhimmanci mutane su ke ankararwa inda suna da shakku, kuma ta yi murna da goyon-bayan da ta samu daga gidauniyar 'Stop it Now'.

'Gane alamomi'

Lambar kar-ta-kwana ta farko da ke boye bayanan mutane da aka samar domin kare cin zarafin yara ta hanyar taimakawa damuwar da manya ke nunawa da tunani kan dabi'u da neman yara.

Shugaban gidauniyar Donald Findlater ya umarci duk mutumin da ya fahimci abokin zamansa ko ɗan uwa na kallon hotunan batsa na yara ƴan kasa da shekaru 18 ya kira lambar kai tsaye.

"Saboda annobar korona da aiki kut da kut da zama tare a gida. Ina ganin su suka taka rawa wajen ƙaruwar da muka samu na amsa waya a wannan layin.

"Mutane wataƙila sun sanya ido sosai ko kuma sun fahimci abin da masoyansu ke aikatawa,"a cewarsa.

A shekarar 2020, mutum 114 daga Wales sun tuntubi wannan lamba ta kar-ta-kwana kan nasu dabi'un ko waɗanda suke tare, mutum 2,700 kuma sun ziyarci shafinmu na samun bayanai da kanka.

Mr Findlater ya ƙara da cewa: "Saboda annobar korona, tunanin kaɗaici, gajiya da rashin tabbas, musamman a tsawon shekarar da ta gabata, na daga cikin abin da ya jefa akasari masu kiramu cikin wannan mumunan dabi'a, da aikata haramtattun dabi'u a shafukan intanet.

"Akwai sarƙaƙiya wajen gano alamomin amma sun haɗa da, kasancewa mai sirri a na'urorin shiga shafin intanet, yin abubuwa a lokuta bambarakwai - kamar tashi da sanyin safe da yin abu kamar mara gaskiya ko rashin samun natsuwa."

Sashin kare haƙƙin yara na ma'aikatar ƴan sanda a Burtaniya ya ja hankalin mutane kan ankararwa idan suka fahimci wata alama ta cin zarafi ko tunani mara kyau a kan yara tsakanin iyalansu, sannan suna shawartar a tuntubi gidauniyar 'Stop It Now.'

Source: BBC