Menu

Yadda rashin makewayi ke hana yara mata karatu a Sokoto

 117541834 Img 8695 Sokoto na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar karancin sanya yara mata makaranta

Sun, 14 Mar 2021 Source: BBC

Rashin sanya yara mata makaranta wani kalubale ne da ya dade yana addabar yankin arewacin Najeriya.

Duk da cewa rahotanni na nuna cewa ana samun ci gaba wurin sanya yara makaranta amma har yanzu akwai wadansu matsaloli da ke yin cikas ga karatun na yara mata a jihohi daban-daban na kasar.

Sokoto na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar karancin sanya yara mata makaranta, duk kuwa da cewa gwamnatin jihar ta ce tana bakin kokarinta wurin inganta karatu.

Bayan hawa kan mulki a shekara ta 2015, gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana dokar ta-baci a kan ilimi tare kuma da kafa wani asusu na ra'aya bangaren na ilimi karkashin jagorancin mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad.

A wata tattaunawa da BBC gwamnan ya ce sun yi kujeru sama da dubu 150 wadanda aka rarraba a makarantun jihar Sokoto.

Ya kuma ce gwamnatinsa karkashin hukumar kula da ilimin firamare ta kashe kudi sama da Naira biliyan 10 wurin ginawa da gyara makarantun firamare.

Sai dai da alama har yanzu har yanzu wadannan ayyuka ba su kai wasu yankunan jihar ba.

BBC ta kai ziyara a wata makarantar firamare da ke kauyen Tuntube da ke karamar hukumar Dange Shuni.

Tuntube, kauye ne da ke da nisan kimanin klm 10 daga birnin Sokoto.

Ginin makarantar firamaren da ke kauyen ya tsatssage, haka nan kuma wani bangare ya rushe.

Sani Bahago shi ne shugaban kungiyar iyaye da malamai na makarantar firamaren, ya ce "Muna neman a taimaka mana saboda a gyara mana koda gini daya ne, domin gini uku na makarantar sun ruguje."

Gini daya ne kawi mai lafiya a makarantar, inda nan ne dalibai ke amfani da shi wajen karatu, abin da ya sanya da yawa daga cikin iyaye ba su tura yaransu zuwa makarantar.

Haka nan kuma rashin kyauren kofa da na taga na sanya yara rashin zuwa makarantar a lokacin damina da kuma lokacin sanyi.

Kulu Umaru wata uwa ce da take da yara mata a makarantar, sai dai ta ce rashin ban-daki na daga cikin abinda ke hana dalibai mata zuwa makarantar.

Ta ce "Ina da 'ya a wannan makarantar kuma ina so ta yi karatu, amma saboda babu makewayi koda sun zo makarantar sai dai su je makwafta idan za su zagaya, shi ya sa wani lokaci ko mun turo su sai su ce za su zo saboda babu makewayi."

Makewayi biyu ne a makarantar ta Tuntube, sai dai rufin makewayin ya fita, babu kofa, sannan kuma ciyawa ta cika bayin.

Attahiru Muhammad wani magidanci ne da ya cire yaransa daga makarantar.

Saifullahi dalibi ne a makarantar ya ce "Muna zama a cikin wannan aji, babu taga, gini ya tsattsage, muna tsoron kada gini ya fado mana.

Hon. Bello Muhammad Gwiwa shi ne kwamishinan ilimi na Jihar Sokoto, y ace lalacewar makarantu ba sabon abu ba ne a Najeriya, sai dai ya ce gwamnatin jihar Sokoto na iyakar bakin kokarinta wajen ganin ta gyara makarantu.

A shekarar da 2020 hukumar ilimin bai daya ta jihar Sokoto ta amabato gwamnan Aminu Tambuwal na cewa gwamnatinsa ta narkar da tsabar kudi Naira biliyan 19 a cikin shekara 5 domin ginawa da kuma gyara makarantu a fadin jihar.

Wannan rahoto ne na musamman da BBC Hausa ke kawowa tare da tallafin gidauniyar MacArthur.

Source: BBC