Yajin aikin da uwar kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kira na tasiri a asibitoci gwamnati da dama da ke fadin Najeriya.
Kama daga jihar Ogun zuwa Delta da Kaduna, yajin aikin ya kawo cikas ga ayyuka a asibitocin gwamnati.
Likitoci a wasu asibitoci da ke jihar Legas su ma sun amsa kiran da uwar kungiyar ta NARD ta yi musu.
Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa a asibitin gwamnatin na Luth da ke Legas, Dr Oluwafemi Hassan ya ce likitocin za su koma bakin aiki ne idan gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Ya kuma ce shugabannin kungiyar za su ci gaba da tattaunawa da gwamnatin kasar a ranar Talata, bayan an kammala hutun easter.
Likitocin sun nemi a biyasu dukkanin albashi da alawus-alawus da suke bin gwamnati.
Sai dai a dayan bangaren, gwamnatin kasar ta yi barazanar aiwatar da tsarin 'ba aiki ba bu albashi' idan likitocin suka ki komawa kan teburin shawara.