Menu

Yan Biafra: Yadda masu son ballewa daga Najeriya suka ‘kashe Hausawa 12 a Imo’

 105914308 Dzccrkmwwaeg7zm Tsohon shugaban yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu

Tue, 6 Apr 2021 Source: BBC

Rahotanni daga jihar Imo a Kudu maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa mutum uku sun hallaka bayan wani hari da ake zargin Kungiyar mayakan Biafra ta kai wa al'ummar Hausawa da ke yankin Orlu a jihar.

Al'amarin dai ya jefa al'ummar Hausawan da ke yankin cikin zaman zulumi.

A cewar wani dan kasuwa Bahaushe mazaunin yankin na Orlu, Alhaji Amadu Ali, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu, kungiyar ta Biafra ta halaka Hausawa 12 baya ga asarar dukiya ta kusan naira miliyan 42 da suka tafka.

"Mu dai mun tashi kawai ranar Laraba, wani mai nama, yana tafiya ya dawo da wuri kawai ya haɗu da waɗan nan mutanen suka buɗe masa wuta, abin da suka sakar masa harsashi na AK47, ya mutu", in ji Alhaji Ahmadu Ali.

Ya fadawa BBC cewa lamarin ba mai naman kadai ya shafa ba har da wani ɗan sarkin gari da shi ma yake sayar da mana wanda suka halaka shi.

Dan kasuwar ya ce ba zai iya bayyana wani dalili da ya sa yan Biafran suke kai musu hari ba "don bamu da fada da kowa, ba mu da tsokana da kowa".

"Tun daga ranar da aka yi (rikicin) Endsars suka fara kashe mutanenmu ɗaya bayan ɗaya", in ji Alhaji Amadu Ali.

Ya ce kawo yanzu, yan Biafran ba su fara bi gida-gida ba amma suna kai hari ne kan masana'antun Hausawa inda suke harbe su.

Ya yi ikirarin cewa hukuma tana sane da abin da ke faruwa a jihar saboda "ƴan sanda su suka bamu motar da muka dauki gawar mutum uku muka bizne kuma sai da kwamishinan ƴan sanda ya yi magana a bamu gawar sannan aka bamu".

Source: BBC