Manchester City za ta karbi bakuncin Manchester City a wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Talata a Etihad.
A wasan farko da suka buga a Faransa ranar 28 ga watan Afirilu, City ce ta yi nasara da ci 2-1.
Wannan shi ne wasa na biyar da za su fafata a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda City ta yi nasara a biyu da canjaras biyu.
City wadda take ta daya a teburin Premier ta lashe Caraboa Cup na bana na hudu a jere kuma na takwas jumulla.
Paris St Germain tana ta biyu a kan teburin Ligue 1 da maki 75 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille wadda ke jan ragama.
Wannan ne karon farko da Pep Guardiola ya kai wannan matakin a Champions League a Manchester City, wadda ba ta taba lashe kofin ba.
A bara PSG ta kai karawar karshe a Champions League, inda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Bayern Munich.
'Yan wasan Paris St Germain: