Bayern Munich ta ziyarci Paris St Germain domin buga wasa na biyu na daf da karshe a quarter final a Champions League ranar Talata.
Kungiyoyin sun kara a wasan farko ranar Laraba a Jamus, inda PSG ta yi nasara da ci 3-2.
Bayern ta kai hari 31 a ragar PSG, inda 12 daga ciki suka nufi raga kai tsaye, ita kuwa kungiyar Faransa guda shida ta samu.
Joshua Kimmich ya kirkiri damarmaki 10 a wasan, kuma bajintar da aka yi a Champions League a quarter finals tun bayan wadda Mesut Ozil ya yi a Real Madrid a wasa da Tottenham a Afirilun 2012.
Bayern ta lashe Champions League karo shida har da wanda ta doke PSG a bara da ci 1-0, ita kuwa kungiyar Jamus ba ta taba daukar kofin ba.
Lewandowski ya ci kwallo 42 a wasannin da ya buga wa Bayern Munich a kakar bana, daga baya ya yi rauni bai fuskanci PSG a Jamus ba.
'Yan wasan PSG da ke taka leda a Bayern:
Coman da Choupo-Moting da kuma Tanguy Nianzou.
'Yan kwallon Bayern da ke PSG:
Draxler da Diallo da Thilo Kehrer da kuma Bernat.
'Yan wasan Paris St Germain:
Mauro Icardi ya koma yin atisaye yana ta faman ya samu kuzari a jikinsa.
Layvin Kurzawa shima ya koma atisaye amma sai ranar Alhamis zai ci gaba da karbar horo cikin 'yan kwallo.
Shi kuwa Juan Bernat na ci gaba da yin jinya.