Sojojin Ethiopia sun kama wakilin BBC a yankin arewacin Tigray mai fama da rikici.
Girmay Gebru, wakilin sashen BBC Tigrinya, an kama shi ne tare da wasu mutum huɗu a wani wurin shan gahawa a Mekelle babban birnin yankin.
Shaidu sun shaida wa BBC cewa sojoji ne sanye da kakin soja suka kama mutanen biyar suka tafi da su cikin ayarin motocin soja.
Ba a san inda ake tsare da su ba kawo yanzu. BBC ta samu rahotannin da ke cewa an tafi da wakilinta a wani sansanin soji a Mekelle.
Yankin Tigray ta kasance ƙarƙashin ikon sojoji tun watan Nuwamban bara, lokacin da Firaministan Habasha ya sanar da cewa dakarun ƙasar sun ƙwace ikon yankin bayan ƙaddamar da farmaki kan ƴan tawayen Tigray.