Yawan al'umma a China ya ragu sosai cikin shekaru, a cewar kididdigar da gwamnatin kasar ta fitar ranar Talata.
Karuwar da aka samu a shekara ta kai kashi 0.53 cikin shekara 10 da ta gabata, kasa da kashi 0.56 cikin 100 tsakanin shekarar 2000 zuwa 2010 - abin da ya sa adadin ya kai mutum 1.41bn.
Kididdigar ta kara matsa lamba kan China ta samar da matakan da suka shafi ma'aurata su kara haihuwa domin rage matsalar raguwar yawan al'umma.
Ana samar da sakamakon ne a kidayar da ake sau daya cikin 10 wanda tun farko ake tsammanin za a fitar cikin watan Afrilu.
An yi kidayar ne a karshen shekarar 2020 inda jami'an kidaya kimanin miliyan bakwai suka bi gida-gida domin karbar bayanan al' ummar China.
Abin da muka sani game da yawan haihuwa a ChinaShugaban hukumar kididdiga ta kasar, Ning Jizhe, ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata, an haifi jariri miliyan 12 - an samu koma-baya idan aka kwatanta da jariri miliyan 18 da aka haifa a 2016.
Mr Ning ya kara da cewa karancin haihuwa shi ne dalilin da ya haifar da ci gaban tattalin arziki a China.
Yayin da kasashe ke kara samun ci gaba, ana samun raguwar haihuwa saboda ilimi ko wasu abubuwan da aka fi fifitawa kamar aiki.
A kasashen makwabta Japan da Koriya ta Kudu, misali suma sun fuskanci karancin haihuwa a shekarun baya-bayan nan duk da irin tagomashin da gwamnati ke bai wa ma'aurata don su kara haihuwa.
A shekarar da ta gabata, an samu yawan mace-mace a Koriya ta Kudu fiye da haihuwa a karon farko a tarihi abin da ya ja hankali a kasar da tuni a duniya ta fi fuskantar raguwar haihuwa.
Raguwar yawna al'umma matsala ce saboda shekaru - tsoffi sun fi yawa a kan matasa.
Idan hakan ta faru, za a samu karancin ma'aikata a gaba da za su tallafawa tsoffin sannan za a samu karuwar mutanen da ke neman kulawa a asibiti.
Shin China tana yin wani abu na inganta haka?
A 2016, gwamnati ta kawo karshen tsarin nan na haihuwa sau daya da ke cike da takaddama inda ta bai wa ma'aurata damar haihuwar yara biyu.
Amma tsarin bai magance matsalar rashin haihuwa ba duk da karin shekara biyu da aka yi daga baya.
Ms Yue Su, wata masaniyar tattalin arziki daga sashen kula da bayanan da suka shafi tattalin arziki, ta ce: "Duk da cewa tsarin haihuwa na biyu ya yi tasiri amma na gajeren zango ne."
An yi tsammanin cewa China na iya soke shirin nan na tsara iyali da kuma sabon sakamakon kidayar amma hakan bai faru ba.
Wani rahoto da jaridar Financial Times a farkom watan Afrilu ya ambato mutane da ke da masaniya suna cewa kidayar za ta nuna raguwar da aka samu a yawan al'umma.
Hakan ba ta faru ba a rahoton 2020 amma kwararru sun fada wa kafafen yada labarai cewa hakan na iya faruwa cikin shekara biyar a gaba.
"Zai faru a 2021 ko 2022 ko ma nan kusa," in ji Huang Wenzhang, wani kwararre kan nazarin yanayin kasa a cibiyar harkokin China da Duniya.
Yawan al'ummar China na tafiya ne bisa tsarin tsarin haihuwa sau daya da aka bijiro da shi a 1979 domin rage yawan jama'a.
Iyalan da suka saba dokar sun fuskanci hukuncin biyan tara da rashin aikin yi da kuma tilasta zub da ciki.
Me kuma muka koya?
Yawan mutanen da suke aiki - wanda ya hada mutane yan shekara tsakanin 16 da 59 - shi ma ya ragu da miliyan 40 sabanin kidayar da aka yi a 2010. Amma masani Zeng Yuping ya ce har yanzu yawan al'ummar na da girma inda ake da miliyan 880.
"Har yanzu muna da ma'aikata masu yawa," in ji shi.
Sai dai masaniyar tattalin arziki Ms Yue ta yi gargadin cea nan gaba, ci gaba da samun raguwar ma'aikata zai takaita bunkasar tattalin arzikin China.