Menu

Yin aiki na dogon lokaci ya kashe mutum 745,000 a shekara ɗaya - WHO

 118550018 20210517 184446 Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce yanayin zai ƙaru saboda annobar korona

Tue, 18 May 2021 Source: BBC

Yin aiki na dogon lokaci na sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane duk shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Binciken na farko da aka gudanar a duniya ya nuna cewa mutum 745,000 suka mutu a 2006 sakamakon mutuwar ɓarin jiki da matsalar zuciya saboda yawan lokacin da suka kwashe suna aiki.

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce yanayin zai ƙaru saboda annobar korona.

Binciken ya gano cewa an fi alaƙanta mutuwar ɓarin jiki da shafe awannin aiki 55 a mako ɗaya da kashi 35 yayin da kuma kashi 17 suka fi shafar matsalar zuciya, idan aka kwatanta da awannin aiki 35 a mako ɗaya zuwa awa 40.

Binciken wanda Hukumar Ƙwadago ta Duniya (ILO) ta gudanar, ya nuna kusan kashi ɗaya bisa huɗu na waɗanda suka mutu sakamakon yawan awannin aiki, masu matsakaitan shekaru ne ko kuma manya.

Yawanci, ana samun mace-macen ne daga baya, wani lokaci bayan shekaru da dama fiye da awannin da aka shafe ana aiki.

Makwanni biyar da suka gabata, wani saƙo da wani ɗan shekara 45 Jonathan Frostick ya wallafa a LinkeIn ya ja hankali kan batun yawan awannin aiki.

Mutumin wanda manaja ne a Bankin HSBC ya zauna a ranar Lahadi da yamma domin shirya ayyukansa na mako kafin ya fara jin gajiya a ƙirjinsa da kuma matsala a maƙogaro da kuma matsalar yin numfashi.

"Na tashi na hau gado domin na kwanta, lamarin da ya ja hankalin matata wacce ta kira lambar 999," in ji shi.

Yayin da da yake farfaɗowa daga ciwon zuciya, Mr Frostick ya yanke shawarar sake yin nazari kan yadda zai tunkari aikinsa. "Ba zan sake shafe yini ba a Zoom," in ji shi.

Saƙonsa ya ja hankali inda ɗaruruwan mutane suka karanta, tare da bayar da nasu labarin kan yawan aikin da suke da kuma illarsa ga lafiyarsu.

Mr Frostick mai ɗora laifin yawan lokacin da yake shafewa yana aiki ba kan waɗanda yake yi wa aiki, amma ya bayyana cewa: "Kamfanoni suna kai mutane ga bango ba tare da sun damu da rayuwarsu ba."

HSBC ya ce dukkanin ma'aikatan bankin suna yi wa Mr Frostick fatan murmurewa cikin gaggawa.

"Muna sane da muhimmancin lafiya da kuma jin daɗi da walwala da daidaito a wajen aiki. A tsawon shekarar da ta gabata mun linka ƙoƙarinmu ga lafiya da kuma jin daɗin ma'aikata.

"Yadda wannan ya ja hankali ya nuna yadda matsalar ke ci wa mutane tuwo a ƙwarya, kuma muna ƙarfafawa mutane gwiwa su dinga ɗaukar lafiyarsu da walwalarsu a matsayin abin da ya fi muhimmanci."


Yayin da binciken bai shafi lokacin da ake cikin annobar korona ba, jami'an WHO sun ce ƙaruwar yin aiki daga gida da taɓarɓarewar tattalin arziki ya ƙara haifar da bazanaar matsaloli da ke da nasaba da yawan awannin aiki.

"Muna da wasu hujjoji da ke nuna yadda idan aka sanya dokar kulle a wata ƙasa, yawan awannin aiki na ƙaruwa da kusan kashi 10, a cewar jami'in WHO Frank Pega.

Rahoton ya ce yin aiki na tsawon awanni an kiyasta cewa shi ne musabbabin kusan ɗya bisa uku na cututtukan da ake samu a wurin aiki, wanda ita ce matsala mafi girma da ta shafi aiki.

Masu binciken sun ce akwai hanyoyi biyu na awannin aiki da yawa da suke kai wa ga matsaloli na lafiya:

Na farko shi ne matsalar da ke da nasaba da damuwa, na biyu kuma shi ne yawan shan taba sigari da giya zai ƙaru sakamakon awannin da ma'aikata ke shafe wa suna aiki, sannan babu wadataccen bacci da motsa jiki da kuma samun abinci mai gina jiki.

Yawan mutanen da ke aiki na tsawon awanni ya ƙaru kafin ɓullar annobar korona, kuma kusan kashi tara na yawan jama'ar duniya, in ji WHO.

A Birtaniya, ofishin hukumar ƙididdiga ya gano cewa mutane da ke aiki daga gida lokacin annobar korona na ƙara akalla awa shida a mako da ba za a biya su ba.




WHO ta bayar da shawara ga kamfanoni da hukumomi su dinga nazari kan lafiya da matsalolin ma'aikatansu.

Keɓe awanin hutu za su yi matukar tasiri domin zai ƙara ingancin aiki, in ji Mr Pega.

"Zai kasance zaɓi mai kyau kada a ƙara yawan lokacin aiki a lokacin da ake cikin matsalar tattalin arziki."

Source: BBC