Menu

Za a buga daf da karshe a Champions cikin Afirilu da Mayu

Champions League Logo Real Madrid ta lashe Champions League karo 13, Chelsea sau daya; City da PSG basu taba dauka ba

Fri, 16 Apr 2021 Source: BBC

An samu kungiyoyi hudun da za su buga karawar daf da karshe a gasar Champions Leauge ta bana.

Real Madrid wadda ita kadai ce daga Spaniya ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi nasara a kan Liverpool da ci 3-1 gida da waje.

Paris St Germain wadda ta buga wasan karshe a bara za ta yi fafatawar daf da karshe a wasannin bana, ita ce ta fitar da Bayern Munich mai rike da kofin.

Chelsea wadda ke taka rawar gani tun bayan da Thomas Tuhel ya karbi jan ragama a watan Janairu ta yi waje da Atletico Madrid da FC Porto.

Manchester City kungiya ta biyu daga Ingila karkashin Pep Guardiola ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi nasara a kan Borussia Dortmund da ci 4-2 gida da waje.

Real Madrid ta lashe Champions League karo 13, Chelsea ta dauka sau daya, yayin da Paris St Germain da Manchester City ba su taba cin kofin zakarun Turan ba.

Ranakun da za a buga wasan daf da karshe a Champions League:

Za a buga zagayen farko tsakanin 27 ko kum,a 28 ga watan Afirilu, inda Real Madrid da Paris St Germain ke gida.

A makon gaba kuwa Chelsea da Manchester City ne za su karbi bakuncin karawa ta biyu.

Real Madrid da Chelsea: Talata 27 ga Afirilu ko kuma Laraba 28 ga Afirilu

Chelsea da Real Madrid: Talata 4 ga Mayu ko kuma Laraba 5 ga Mayu

PSG da Manchester City: Talata 27 ga Afirilu ko kuma Laraba 28 ga Afirilu

Manchester City da PSG: Talata 4 ga Mayu ko kuma Laraba 5 ga Mayu

Source: BBC