Menu

Za a bukaci ma'aikatan bankuna su bayyana kadarorinsu a Najeriya

 117600257 7ba1d5fa 3fff 4dc3 90fb 7fe9c076182d Shugaban EFCC, Abdulrashed Bawa

Wed, 17 Mar 2021 Source: BBC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya (EFCC) ta ce nan ba da jimawa ba za ta nemi masu gudanar da harkar hada-hadar kudi a Najeriya, musamman ma bankuna da su bayyana kadarorinsu daga ranar 1 ga Yunin 2021.

Shugaban EFCC, Abdulrashed Bawa, ya ba da wannan umarnin ne a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Wata jaridar cikin gida ta ambato shi yana cewa, hukumar ta damu da irin rawar da cibiyoyin kudi ke takawa wajen taimaka wa wadanda ke aikata laifuka wajen samun kudaden da suka sace.

    AbdulRasheed Bawa: Buhari ya nada shi a matsayin sabon shugaban EFCC EFCC: Tsoffin jami'an gwamnatin Najeriya da za a tuhuma a shekarar 2021 Rashawa: Manyan jami'an Najeriya shida da suka yanke jiki suka faɗi yayin tuhumarsu
"Daga ranar 1 ga watan Yuni, EFCC, za ta bukaci bankuna su soma aiki da fom din bayyana kadara, wanda masu bankin suka cike domin mu tabattar bankunan suna biyayya da layin da muka zana daga 1 ga Yuni" in ji Abdulrasheed Bawa.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ta kuma ambato Mista Bawa yana cewa matakin na karkashin dokar Ma'aikatan Bankin ta ETC da aka zartar a 1986, wadda aka kafa domin tabbatar da wani tsari da zai yi yaki da masu almundahana a fannin hada hadar kudaden kasar.

Ya kara da cewa daukar matakin zai kuma taimaka wajen toshe wasu hanyoyin da ake amfani da su a halin yanzu wadanda wasu bata gari ke amfani da su a fagen don kawo nakasu ga tattalin arzikin Najeriya ta hanyar halatta kudin haram da hada-hadar kudade ta hamramtacciyar hanya.

Source: BBC