Ana sa ran cimma yarjejeniya a karshen watan nan kan sauya fasalin gasar Champions League zuwa kungiya 36 daga gasar 2024.
Shugaban kungiyoyin kwallon kafar Turai, Andrea Agnelli na sa ran za a fitar da tsarin da ya kamata a raba gurbi hudun karin kungiyoyin da aka samu a wasannin.
Ana sa ran kulla yarjejeniya da zarar an yi taro tsakanin shugabannin kungiyoyin kwallon kafa da hukumar kwallon kafar Turai.
Agnelli, wanda shi ne shugaban Juventus ya bayar da tabbaci kan yadda ake daf da kulla yarjejeniyar sabon fasali a Champions League.
Tun farko babban jami'in Ajax, Edwin van der Sar, shi ne ya bayar da shawarar yadda ya kamata a sauya tsarin da ake yi a Gasar ta Zakarun Turai.
Maimakon tsarin kungiya hudu a kowanne rukuni takwas da ke wasa shida, yanzu dukkan kungiyoyin za su yi karawa 10 a tsakaninsu.
Da haka za a tanadi teburin da zai fayyace wadanda za su kai wasan daf da na kusa da na karshe sannan su kara gida da waje.
An kuma bayar da shawarar cewar sauran gurbi hudun da za a kara a wasannin ya kamata a waiwayi kananan kasheshe, domin suma a basu damar shiga gasar ta Turai.