Menu

Zaɓen 2023 : Ya kamata miƙawa ƴan kudu mulki a 2023 - Ndume

 117588598 Alindume Wasu Jiga

Thu, 18 Mar 2021 Source: BBC

Wasu jiga-jigan jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya sun fara yin kiran ya kamata jam`iyyar ta keɓe takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023 ga yankin kudancin ƙasar.

Masu irin wannan ra`ayin na cewa yin hakan shine adalci ga kudancin ƙasar, tunda ɗan arewa, wato shugaba Muhammadu Buhari ne ya samu wa`adin mulki biyu a ƙarƙashin tutar jam`iyyar, don haka sake tsayar da ɗantakara daga yankin arewa zai zamanto tauye haƙƙin ƴan kudu.

Senata Mohammed Ali Ndume, ɗan majalisar dattawan ƙasar ne mai irin wannan ra`ayin, kuma ya shiadawa BBC cewa ya kamata ya kasance an gina jam'iyyar APC a kan adalci, irin wanda aka yi lokacin da aka nemi arewa ta bayar da ɗan takara.

A cewarsa, ''Haka aka yi har aka goyi bayan shugaba Muhamadu Buhari, mutum ɗaya ne daga kudu wato Rochas Okorocha ya fito daga kudu, kuma shima ya fito ne a ra'ayin kansa ba tare da goyon bayan jam'iyya ba, shi yasa ma bai samu nasara ba''.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi idan an zo zaɓen 2023 a ramawa kura aniyarta, ma'ana a goyawa kudu baya domin ta bayar da nata ɗan takarar, ''Daga nan sai muga abin da Allah zai yi'' inji Sanata Ndume.

    Sabuwar ɓaraka ta kunno kai a jam'iyyar APC kan zaɓen 2023 Ko Tinubu na sansana kujerar shugaban kasa? 'Har yanzu APC ba ta cika jam'iyya ba'
Sai dai a cewarsa, babu ta yadda za su goyi bayan masu neman raba ƙasa su shugabanci Najeriya, don haka duk ɗan takarar da zai fito daga kudu, al'ummar arewa za su duba wanda zai kare muradun yankin ne.

''Waɗanda basu yarda da hadin kan kasar nan ba bazasu samu goyon bayan yan arewa ba, don babu ta yadda za a amince da mai son a wargaza gida ya jagoranci gidan'' a cewar Ndume.

Ita dai jam'iyyar APC ta ce ba a kai lokacin da ya kamata a fara tattauna wannan batu ba, amma wasu gagganta irinsu Sanata Ali Ndume na ganin cewa da zafi zafi a kan bugi ƙarfe, don haka suna magana ne tun kafin a kai ga lokacin da za a kasa fahimtar juna.

Yayin da shekaru kusan uku suka rage a gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya wasu rahotanni na nuni da cewa tuni masu sha'awar tsayawa takara a jam'iyyar daga dukkan yankuna ciki har da arewa, suka fara wasa wuƙaƙensu don ganin sun samu goyon baya ƴan jam'iyyar.
Source: BBC