Menu

Zaben Iran: Su waye ƴan takarar shugaban ƙasar?

 118698814 Gettyimages 1232919482 1 Shugaban Iran Hassan Rouhani

Sat, 29 May 2021 Source: BBC

An bai wa mutane bakwai damar tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar Iran da za a gudanar wannan watan.

Ɗaruruwan mutane sun yi rijistar tsayawa takarar amma hukumar zaɓe ta the Guardian Council ta soke su. Cikin waɗanda aka amince da su, biyar masu tsattsauran ra'ayi ne.

Sauran biyun kuma masu matsakaicin ra'ayi ne - wato ra'ayinsu kan ƙasashen Yamma bai fiye tsauri ba - sannan akwai mai son kawo sauyi ɗaya, ko kuma wanda ra'ayinsa dangane da ƴanci ɗan Adam da diflomasiyya ke da sassauci.

Ga jerin 'yan takarar:

Mai farin jini: Ebrahim Raisi

Mutane da yawa na ganin cewa an share wa mutum ɗaya fagen yin nasara: Ebrahim Raisi, shugaban ɓangaren shari'a na Iran kuma mai tsattauran ra'ayi, wanda ake gani a matsayin na gaba-gaba wajen gadar ba Shugaba Hassan Rouhani kawai ba, mai yiwuwa har Jagoran Addini Ayatollah Ali Khamenei.

Duk sauran ƴan takarar shida ba su da wannan damar.

Ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa da alƙawuran yaƙi da "yanke ƙauna" da matsin tattalin arziƙi ya haifar a ƙasar.

Mista Raisi na da gagarumin goyon baya a ɓangaren masu ra'ayin ƴan-mazan-jiya kuma ana sa rai zai yio nasara ba tare da wasu ƙalubale ba bayan da aka hana wasu ƴan takarar da ka iya yin tasiri a takarar.

Ya fara aiki da ɓangaren shari'a bayan juyin juya halin 1979 kuma ya yi aiki a matsayin mai shigar da ƙara a mafi yawan shekarun aikinsa, inda ya riƙa janyo ce-ce-ku-ce.

Yana cikin wani kwamiti na musaman da ya yi aiki kan kisan wasu fursunonin siyasa da dama a 1988 yayin da yake aiki a matsayin mataimakin mai shigar da ƙara a Babbar Kotun Musulunci a Tehran.

Haka kuma, ya yi aiki a matsayin mai kula da AStan-e Qods Razavi, wurin bautar shugaban Shi'a na takwas Imam Reza a Mashhad, kuma gidauniya mafi arziƙi a Iran. Sannan shi mamba ne na Majalisar Ƙwararru wadda ke da alhakin naɗawa da cire Jagoran Addini.

Soja: Mohsen Rezai

An naɗa tsohon soja Mohsen Rezai mai shekaru sittin da shida a matsayin kwamanda na Rundunar tsaron ƙasar ta Islamic Revolutionary Guard Corps a 1981 kuma ya jagorance ta a lokacin yaƙin Iran da Iraƙi a 1980.

Ya tsaya takarar shugaban ƙasa sau uku kuma bai taɓa riƙe wani muƙami a gwamnati ba. Sannan bai yi nasarar shiga majalisar dokokin ƙasar a 2000 ba. Ana yi masa inkiya da "dan takarar da ba ya gajiya".

Wasu sun soki matakansa lokacin yaƙin Iran da Iraƙi, inda suka ce ya ɗauki shawarwarin da suka janyo mutuwar sojoji da tsawaita yaƙin - zarge-zargen da ya musanta.

Mista Rezai yana da digirin digirgir a fannin tattalin arziki daga Jami'ar Tehran.

Mia faɗa a ji: Saeed Jalili

Saeed Jalili ya yi fice a matsayin babban mai shiga tsakani kan nukiliyar Iran daga 2007 zuwa 2013, lokacin shugabancin Mahmoud Ahmedinajad, lokacin yana mataimakin ministan harkokin waje.

Jagoran Addini Khamemei ne ya naɗa shi kan duk wani muƙami da yake riƙe da shi a halin yanzu, matasa masu tsattauran ra'ayi na ganin Mista Jalili a matsayin wani ɓangare na "masu faɗa a ji". Magoya bayansa sun ce ana sukarsa ne "saboda ƴancin tunaninsa da rashin sa hannu a cin hanci da rashawa".

Yana da ikon faɗa-a-ji a matsayinsa na mamba na Majalisar da ke bai wa Jagoran Addini Shawarwari kan duk wani rikici da majalisar dokoki.

Shi ma ya taɓa tsayawa takara a baya, inda ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2018.

Mai son kawo sauyi ɗaya tilo: Mohsen Mehralizadeh

Mohsen Mehralizadeh shi ne ɗan takara ɗaya mai son kawo sauyi a zaɓen. Sai dai, yana takarar ne ba a ƙarƙshin ko wace jam'iyya ba. Ba a sa sunansa a jerin Reforms Front ba, wani haɗin gwiwar jam'iyyu da ƙungiyoyi 27 masu son kawo sauyi, waɗanda Guardian Council ta soke ƴan takararsu tara.

Ba a san dalilin da ya sa aka ware Mista Mehralizadeh ba daga cikin sauran masu son kawo sauyin a zaɓen.

An ƙi amincewa da buƙatarsa ta son shiga zaɓen 2005 kafin daga baya Ayatollah Khamenei ya ba shi damar tsayawa. Amma a 2016 an sake haramta masa tsayawa takarar majalisar dokoki.

Masu son kawo sauyin ba su da farin jini a halin yanzu. Ƴan Iran da yawa waɗanda suka zaɓi wannan gwamnatin suna takaici tare da zargin gwamnatin da hannu a matsalolin tattalin arziƙin da ƙasar ke ciki, waɗanda suka ƙaru bayan da Amurka ta sake ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi bayan da ta fice daga yarjejejiyar nukiliyar Iran ta 2015.

Ƙwararren ma'aikacin gwamnati : Abdolnasser Hemmati

Abdolnasser Hemmati shi ne kawai wanda ba mai tsattauran ra'ayi ba da aka ba damar tsayawa takara baya ga Mista Mehralizadeh. Yana da matsakaicin ra'ayi kuma ƙwararre ne wanda ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan babban bankin ƙasar a 2018.

Shugaba Ahmedinajad da Shugaba Rouhani ne suka ba shi manyan muƙamai, kuma ana iya ganin wannan a ayyukan da yake iya yi da ɓangarorin adawa a siyasar Iran.

Ya fuskanci karya darajar kuɗin iran, da takunkumin Amurka kan ɓangaren bankuna a Iran ciki har da takunkumin da aka ƙaƙaba wa babban bankin da kansa da matsalolin cikin gida kamar kasuwar zuba hannun jari mai rauni da kasuwar kuɗin intanet ta kirifto mai samun tagomashi.

Mista Hemmati na da digirin digirgir a fannin tattalin arziƙi daga Jami'ar Tehran kuma yana koyar da tattalin arziki a jami'ar.

Sauran ƴan takarar

Amirhossein Qazizadeh Hashemi babban likitan fiɗa ne a ɓangaren Kunne da Hanci da Maƙogwaro kuma ɗan majalisa mai tsattsauran ra'ayi wanda ya wakilci yankin Mashhad tun 2008. Haka kuma, shi ne mataimakin kakakin majalisar dokokin ƙasar tsawon shekara guda tun watan Mayun 2020. Mai shekaru 20, shi ne mafi ƙarancin shekaru a ƴan takarar shugabancin ƙasar na bana.

Alireza Zakani shi ma wani ɗan majalisa ne mai ra'ayin ƴan mazan jiya da ya yi fice saboda hamayyarsa ga yarjejejeniyar nukilyar Iran ta 2015. Ya fafata a lokacin yaƙin Iran da Iran kuma a farko-farkon shekarun 2000, ya yi aiki a matsayin kwamandan Rundunar Basij Resistance ta ɗalibai a faɗin ƙasar, rundunar da ke da ikon tabbatar da tsaron cikin gida.

Ya yi ɗan majalisar dokoki na Tehran daga 2004 daga 2016, kuma an sake zaɓen shi a karo na biyu a 2020. Wannan ne karo na uku da zai tsaya takarar shugaban ƙasa. A 2013 da 2017, Guardian Council ta hana shi tsayawa takara.

Source: BBC