Menu

Zaben shugaban kasar Iran: Dalilai hudu da suka sa zaben yake da muhimmanci

 118663381 Mediaitem118663380 Yan Iran za su kada kuri'a a zaben shugaban kasar

Wed, 2 Jun 2021 Source: BBC

A watan nan ne 'yan kasar Iran za su kada kuri'a a zaben shugaban kasar da ke da matukar muhimmanci, a cikin kasar ma ma kasashen waje. Abubuwa da dama sun sauya cikin shekaru hudu tun bayan zaben da aka yi na karshe - ga wasu muhimman dalilai da suka sa ake sanya ido sosai kan zaben.

Rashin gamsuwa

Tun bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2017, abubuwa da dama sun sauya a fannin shiyasar Iran.

Sun hada da musnuga wa masu zanga-zangar kin jinin gwamnati; kama masu rajin kare tabbatar da adalci a siyasa da harkokin yau da kullum, kisan 'yan siyasar da aka tsare a gidajen yari; harbo jirgin kasar Ukraine da Rundunar zaratan sojin Iran ta yi; da kuma matsanancin halin tabarbarewar tattalin arziki da kasar take ciki sakamakon jerin takunkuman karya tattalin arziki da Amurksa ta kakaba mata.

Wadannan matakai sun yi tasiri kan 'yan kasar ta Iran kuma za su yi tasiri kan zaben da ke tafe. Watakila babban abin da zai bai wa masu mulkin Iran haushi shi ne idan masu kada kuri'a ba su fito sosai ba, domin kuwa masu zabe na kololuwar rashin gamsuwa ga masu mulki.

Ko da yake an yi amannar cewa zaben ba zai kasance mai sahihanci ba (galibi saboda hukumar zaben za ta amince ne kawai da wadanda ta ga dama), duk da haka shugabannnin Iran suna bukatar mutane su fito sosai su kada kuri'unsu domin su nuna cewa al'ummar kasar suna goyon bayansu. Batun goyon bayan shi ne babban kalubalen da gwamnati take fuskanta tun daga zaben da aka yi shekaru hudu da suka gabata.

Sai dai wata kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a da kungiyar dalibai ta Iranian Students Polling Agency (Ispa) da ke kusa da gwamnati ta gudanar ta nuna cewa an samu raguwar kashi 7 cikin 36 na mutanen da suka ce za su fito domin su kada kuri'unsu tun da aka fitar da sunayen 'yan takara ranar 20 ga watan Yuni, yayin da aka kirkiri wani maudu'i mai taken "No Way I Vote" wato "Babu Hanyar da zan yi zabe" a shafukan sada zumunta na kasar.

A zabukan da suka gabata, rashi fitowa zabe sosai yana bai wa masu tsattsauran ra'ayi da masu ra'ayin rikau damar samun nasara a zabukan.

Idanu sun karkata kan masu ra'ayin rikau

Tun shekarar 1997, ana samun rabuwar kawuna kan zaben shugaban kasar, tsakanin masu ra'ayin rikau da kuma masu son kawo sauyi.

Sai dai wani umarni da hukumar zaben kasar ta bayar a kwanan baya ya hana akasarin masu son kawo sauyi tsayawa takara a zaben wannan shekarar.

A cikin manyan 'yan siyasa goma da suka yi rijista, bakwai kawai hukumar ta amince su tsaya takara. Biyu daga cikin bakwai din ne kawai suke da sassaucin ra'ayi kuma dukkansu ba su yi suna sosai ba.

Shugaban ma'aikatar shari'ar Iran, Ebrahim Raisi, wanda ya yi takara a zaben 2017, shi ne babban dan takarar da ake sa ran zai yi nasara, kuma a cewar kuri'ar jin ra'ayi jama'a shi ne dan takarar da masu ra'ayin rikau suke so ya lashe zaben.

Wasu masu lura da lamura sun yi amannar cewa sauran mutanen da aka amince su yi takara 'yan rakiya ne kawai da za su taimaka wa Mr Raisi.

Tabarbarewar tattalin arziki

A ko da yaushe tattalin arziki yana taka muhimmiyar rawa a zabukan Iran kuma yanzu ma shi ne babban abin da ke gaban kowane dan takara. Saboda yanayin tattalin arzikin kasar, yanzu Iran na daya daga manyan munanan yanayi game da tattalin arzikinta tun daga shekarar 1979 da aka yi juyin juya hali.

Tasirin da takunkuman da aka kakaba mata suka yi, hadi da na annobar korona, sun sa ta shiga daya daga cikin munanan yanayin tattalin arziki, inda hauhawar farashi ta kai kusan kashi 50.

Lokacin da gwamnati ta kara farashin man fetur a watan Nuwambar 2019 ba tare da yin tuntuba ba, dubban mutane sun yi zanga-zanga a kan titunan fiye da birane 100.

A cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, cikin kwanaki kadan jami'an tsaro sun kashe masu zanga-zanga sama da 300 wadanda ba sa dauke da makamai. Masu zanga-zangar sun bukaci masu rike da madafun iko su sauka daga kan mulkin Iran. Mai yiwuwa irin wannan zanga-zangar ta sake barkewa.

Dangantaka da Amurka

Nasarar da Joe Biden ya yi a zaben Amurka na 2020 ta sanya fata na gari game da yiwuwar farfado da dangantakar difilomasiyya da Iran, bayan zaman doya-da-manja da kasashen biyu suka yi lokacin jagorancin tsohon shugaba Donald Trump. Ko da yake masu ra'ayin rikau a tsakanin 'yan siyasar Iran suna ganin tattaunawa da Amurka ba ta da wani amfani, masu ra'ayin sauyi na ganin hakan yana da muhimmanci.

Kazalika masu sassaucin ra'ayi suna goyon bayan Iran ta shiga kungiyoyin kasashen duniya da ke yaki da halasta kudin haramun irin su Financial Action Task Force (FATF), da sasantawa da Saudiyya da kuma rage kaifin ra'ayi kan Isra'ila.

Irin wadannan matakai za su rage tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankin sannan su bayar da damar farfado da tattalin arzikin Iran da ke cikin mawuyacin hali.

Sai dai a yayin da tsare-tsaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ciki har da na kasashen duniya, suke a karkashin ikon babban shugaban addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, su kuma wadanda suke shirin kaurace wa zaben da ke tafe na shugaban kasa sun yi amannar cewa duk wanda ya zama shugaban kasar ba shi da cikakken iko na sauya tsarin kasar.

Source: BBC