Zimbabwe na yunƙurin kafa wata doka da za ta hukunta waɗanda ake gani "ba 'yan kishin ƙasa ba ne" saboda suna sukar ƙasar idan suka fita ƙasar waje - kuma hakan ya sa masu fafutika ke ɗri-ɗari da ita.
Wani lauya masanin kundin tsarin mulkin ƙasar kuma ɗan adawa, Lovemore Madhuku, ya siffanta dokar a matsayin "mai haɗari", yana mai cewa "babu wata ƙasa da za ta iya fayyace abin da ake nufi da kishin ƙasa".
Duk wanda aka zarga a matsayin maras kishin ƙasa ta hanyar yi wa ƙasar maƙarƙashiya a ƙasar waje game da muradun da take son cimmawa za a tuhume shi da aikata laifi.
Yunƙurin wani ɓangare ne na niyyar gwamnati wajen gyara sunan ƙasar a ƙasashen waje, sai dai 'yan adawa na ganin wata hanya ce ta ƙuntata musu, a cewar Dr Madhuku.
"'Yan gwagwarmaya na yin tafiye-tafiye - mu ne maƙogwaron talakawa kuma muna faɗar gaskiya," a cewar wani ɗan fafutika Rita Nyampinga, wanda ya shafe shekaru a ƙungiyoyin 'yan kasuwa.
"Gwamnati ta daɗe tana rarrashin 'yan ƙasa su yi kishin ƙasa domin haɗ kan ƙasar," kamar yadda wani jami'in jam'iyya mai mulki ta Zanu-PF, Pupurai Togarepi ya faɗa wa BBC.
"Amma bayan an samu jam'iyyun adawa [a 1999] batutuwa da yawa sun taso waɗanda za ka ga kamar ƙasar ta shiga yaƙi.
"Abu ne mai wuya ka iya yin doka kan halayya sannan kuma ba zai yiwu ka kama mutum ba ba tare da wata doka da za ta bayar da damar yin hakan ba."
Halin wariya
Sunan jam'iyyun adawa da ta Zanu-PF mai mulki sun ɓaci a cikin 'yan shekarun da suka gabata.
Dokokin da aka kafa kamar na ƙwace gonakin fararen fata da na yaƙar almubazzaranci da kuma take haƙƙin ɗan Adam, har ma da kisan ɗan gwagwarmaya, sun jawo ƙasashen duniya sun daina hulɗa da Zimbabwe, inda suka ware ta.
Amurka da Tarayyar Turai sun saka wa jagororin jam'iyyar takunkumin tattalin arziki da na balaguro, har ma da manyan sojojin ƙasar game da zargin take haƙƙi da kuma maguɗin zaɓe.
An tuhume su da yi wa gwamnati zagon ƙasa sannan aka zarge su da zuwa neman horo kan ta'addanci da kuma iya sarrafa makamai.
Duk da cewa an sake ta, amma har yanzu tuhumar na kanta, kuma tana fargabar cewa sabuwar dokar za ta sake taƙaita 'yancin faɗar albarkacin baki.
A shekarar da ta gabata, an kama 'yan jarida fiye da 10. Su ma 'yan gwagwarmaya da 'yan adawa an tsare su.