Mutanen da ke cikin mawuyacin halin fama da cutar korona su na cikin hatsarin rasa rayukansu idan su na nahiyar Afirka ne.
Wani bincike da mujallar Lancet ta gudanar ya danganta wannan yanayin ga rashin muhimman kayan da asibitoci ke bukata domin ceto rayuka.
Fiye da mutum 120,000 ne dai su ka mutu daga cutar Covid-19 a Afirka, wanda kimanin kashi 4 cikin 100 na adadin wadanda su ka mutu daga cutar ke nan a fadin duniya.
Wannan ne bincike irinsa na farko da aka yi wanda ke bayyana yawan mace-macen da ake samu a nahiyar daga masu fama da cutar korona.
Mutum 4 cikin 10 da aka kwantar a asibiti a Afirak domin matsananciyar rashin lafiya daga cutar su na mutuwa ne.
Wannan adadin na iya fin haka a asibitocin karkara domin ba su da kayayyakin da ake bukata na magance matsalar.
Fiye da mutum 3,000 daga kasashen Afirka goma ne su ka shiga gwaje-gwajen da aka yi da aya samar da wannan sakamakon rahoton.