BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

La Liga: Benzema ya sake ceto Real Madrid da ƙayatacciyar ƙwallo

 117565188 Gettyimages 1298017475 594x594 Karim Benzema ya ci ƙwallo mai ɗan karen kyau a mintunan ƙarshe

Sun, 14 Mar 2021 Source: BBC

Karim Benzema ya ci ƙwallo mai ɗan karen kyau a mintunan ƙarshe, inda ya ceto Real Madrid daga hannun Elche a wasan La Liga mako na 27.

Real Madrid wadda ta fara wasan na Asabar da tazarar maki takwas tsakaninta da Atletico ta saman teburi, ta sha mamaki lokacin da Dani Calvo ya zira mata ƙwallo a raga a minti na 61.

Benzema ne ya farke ƙwallon bayan wani kurosin da Luka Modric ya yo cikin raga a minti na 73.

Yayin da lokaci ya fara ƙure wa Madrid, ɗan ƙasar Faransan ne ya sake ɗaɗata wata ƙwallo da ta daki tirke sannan ta gangara raga biyo bayan wani wasan ba-ni-in-ba-ka da suka yi da Casemiro.

Da wannan sakamako, Real ta koma matsayi na biyu da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Barcelona, wadda za ta buga nata wasan ranar Litinin da Huesca.

Ita kuwa jagorar teburin, Atelico Madrid, za ta fafata da Getafe a yau Asabar da ƙarfe 9:00 agogon Nijar da Najeriya.

Source: BBC