Mataimakin Shugaban ƙasar Samia Suluhu ne ta tabbatar da mutuwar shugaban
Shugaban Tanzania John Magafuli ya mutu.
Mataimakin Shugaban ƙasar Samia Suluhu ne ta tabbatar da mutuwar shugaban cikin wata sanarwa da aka sanar a kafar yaɗa labaran ƙasar.
A cewar mataimakin shugaban, Mista Magafuli ya mutu ne da yammacin ranar Laraba a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam.
Taarifa ya Kifo Cha Rais Wa Jamhuri Ya Muungano Wa Tanzania pic.twitter.com/LNi5CtoURm
— Samia Suluhu (@SuluhuSamia) March 17, 2021