BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

An samu baraka gabanin zaben shugabannin PDP a arewa maso yammacin Najeriya

 117947705 133130874 3323230067777324 578264239729565179 N Gwamnan Sokoto Tambuwal (hagu) tare da tsohon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

Da alama wata baraka ta kunno kai a reshen jamiyyar PDP na arewa maso yammacin Najeriya, inda daya daga cikin iyayen jam'iyyar a yankin Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan cikin al'amuran jam'iyyar a jihar Kano.

A cewar Kwankwaso wanda yake jagorantar bangaren Kwankwasiyya ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu ƴaƴn jam'iyyar na Kano da ke hamayya da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na yankin Arewa maso Yamma.

"Abin takaici shi ne akwai shi gwamna na Sokoto, wanda a ra'ayinsa bai kamata mu musamman mu yan kKwankwasiyya a bamu wadan nan mukamai ba". in ji Kwankwaso.

To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya musanta wannan zargin inda ya ce "duk wanda yake da sha'awa ya fito ya yi takatra, ya fito ya yi takara".

Ya kuma nisanta kansa da zargin da Kwankwaso ya yi masa cewa yana da hannu a siyawa Sanata Bello Hayatu Gwarzo fom.

Ga karin bayani cikin rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai:



Source: BBC