Ranar Laraba Real Madrid za ta ziyarci Liverpool, domin buga wasa na biyu na quarter finals da za su kece raini a Anfield.
A wasan farko da suka yi ranar Talata a Spaniya, Real ce ta yi nasara da ci 3-1 a gasar ta zakarun Turai.
Liverpool na bukatar cin kwallo biyu domin ta kai zagayen daf da karshe, sai dai golan Real Madrid, Thibaut Courtois ba a taba zura masa kwallo biyu ba a Anfield.
Mai tsaron ragar tawagar Belgium ya fuskanci Liverpool sau shida, wanda ya yi nasara a karawa hudu da canjaras daya aka doke shi wasa daya tal.
Sau hudu ya je Anfield filin da ba a zura masa kwallo biyu a raga BA, wanda ya yi nasara da ci 2-1 sannan karawa uku suka tashi canjaras da ya kama gola.
A Oktoban 2015, Courtois bai buga karawar da Chelsea ta karbi bakuncin Liverpool ba a Stamford Bridge a wasan da Philippe Coutinho ya ci biyu da kungiyar Anfield ta ci 3-1.
Haka kuma bai yi wa Chelsea karawa ta biyu ba a Anfiled da suka tashi kunnen doki 1-1, wanda Eden Hazard ne ya ci wa kungiyar Stamford Bridge kwallon a fafatawar.
A kakar 2014/15 Chelsea ta kara da Liverpool gida da waje, inda suka yi 1-1 a Anfield a wasan daf da karshe a Caraboa Cup.
A wasa na biyu kuwa a Landan kungiyoyin sun tashi karawar ba ci wato 0-0, inda Courtois ya tsare ragar Chelsea.
Courtois wanda ya koma taka leda a Real Madrid a kakar 2018 zai ziyarci Anfield ranar Laraba, kuma idan ya sa kokari kamar yadda ya yi a baya, Real za ta iya kai wa daf da karshe a bana.
Kuma idan har Real ta fitar da Liverpool, za ta fuskanci Chelsea kenan tsohuwar kungiyar Courtois wadda ta ci FC Porto 2-0 a wasan farko a quarter final.