Menu

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Konate da Wenger da Lingard da Aguero, Messi da Odegaard

 118235449 Mediaitem118235448 Ibrahima Konate dan wasan RB Leipzig da Faransa

Wed, 28 Apr 2021 Source: BBC

Liverpool ta zage damtse kan sayen ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 21, Ibrahima Konate a kan kuɗi £40m a wannan kakar, duk da asarar kuɗaɗen harajin da za ta yi na £46m. (Mail)

Kocin Leicester City Brendan Rodgers ba shi da ra'ayin komawa Tottenham domin horar da ƴan wasanta. (Sky Sports)

Hukumar ƙwallon kafar Jamus na tattaunawa da kocin Bayern Munich mai bankwana, Hansi Flick kan maye gurbinsa da Joachim Low a matsayin shugabanta. (90min)

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya nuna cewa a shirye yake ya shiga cikin jeren masu neman rike ƙungiyar irinsu Daniel Ek da wasu tsoffin ƴan wasanta uku. (BeIN Sports, via Mirror)

Ɗan wasan tsakiya a Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, zai tursasa barin Manchester United a wannan kakar idan kwantiraginsa ya kare a West Ham. (Eurosport)

  • Sai a Ingila za a fitar da gwani tsakanin Chelsea da Real
  • Wannan ce kakar da na fi farin ciki a PSG — Neymar
Inter Milan ta shiga sahun masu zawarcin ɗan wasan Manchester City Sergio Aguero, mai shekara 32. Aguero ɗan Argentina zai bar City a wannan kakar idan kwantiraginsa ya ƙare. (Caciomercato - in Italian)

Ɗan wasan Lille da Canada Jonathan David, mai shekara 21, ya ja hankalin Manchester United da Arsenal. (Fichajes.net - in Spanish)

Leeds United ta tattauna kan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Rubin Kazan da Georgia Khvicha Kvaratskhelia, mai shekaru 20. (Football Fancast)

Tottenham ta sanya ido kan ɗan wasan Celtic's mai shekara 22 asalin ƙasar Ivory coast, Ismaila Soro. (Mail)

Mai buga wa Brighton tsakiya kuma asalin Netherlands Davy Propper, ɗan shekara 29, tsohon kulon din sa PSV Eindhoven na farautarsa. (The Argus)

  • Kowacce kasa za ta je gasar nahiyar Turai da 'yan wasa 26
Chelsea ta nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Villarreal Alfonso Pedraza, mai shekara 25, da mai yiwa ƙasar Jamus wasa Robin Gosens, mai shekara 26, da yanzu haka ke taka leda a Atalanta. (Caught Offside)

Tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar Barcelona Jordi Mestre ya ce ɗan wasan gaban Argentine Lionel Messi, mai shekara 33, "zai ci gaba da zama" a kulob ɗin na Sifaniya. (Sin Concesiones, via Talksport)

Real Madrid ba ta da niyyar sayar da ɗan wasanta asalin ƙasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 22. Odegaard yanzu haka na zama aro a Arsenal. (AS - in Spanish)

Har yanzu Arsenal ba ta tattauna da ɗan wasan Brazil David Luiz, mai shekaru 34 ba, kan sabon kwantiragi. (Evening Standard)

Source: BBC