Menu

Jihar Neja: Ana ci gaba da neman mutanen da suka nutse bayan kifewar jirgin ruwa

 118442138 F2faf496 6e1b 4a94 8a01 B8033426b1e8 An ci gaba da jana'izar mutum 28 da suka rasu sababin hadarin

Mon, 10 May 2021 Source: BBC

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya ta ce ana ci gaba da gudanar da aikin ceto, don gano mutum takwas da har yanzu ba a gani ba tun bayan nutsewar wani jirgin ruwa a ranar Asabar.

Tuni dai aka yi jana'izar mutum 28 da suka riga mu gidan gaskiya, sanadin wannan al'amari a kan hanyar zuwa wani ƙauye da ke cikin ƙaramar Hukumar Munya.

Shugaban hukumar Alhaji Ibrahim Inga Ahmed, ya shaidawa BBC cewa jirgin na dauke da mutane 100 da suka fito daga Zumba, suna kan hanyarsu ta komawa gida, kuma lamarin ya faru ne a daf da inda za su sauka, sai jirgin ya daki wani kututtre dake cikin ruwa.

''Sanadin haka ne jirgin ya kife, kuma kawo yanzu an gano mutum 62 a raye, sai guda bakwai da ake ci gaba da nema, da kuma karin wasu 28 da suka riga mu gidan gaskiya'' inji shi.

Ya ce har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da lalube domin tabbatar da cewa an gano mutanen da suka nutse a cikin ruwan.

Lamarin irin wannan na kifewar jirgin ruwa a jihar Neja ba sabon abu bane domin an sha samun haka ko a baya.

Sai dai Alhaji Ibrahim Inga Ahmed ya ce hakan na da nasaba da yawan rafuka da ake da su a jihar kusan a kowanne yanki, kuma suna samuwa ne sanadin dam-dam da ake samarwa, ko kuma da ya ratsa ta jihar.

A cewarsa, tuni gwamnan jihar ya bada umarnin ganin an zauna da matuka jiragen ruwa a jihar domin ganin an samar musu da tallafin da zai taima wajen kare aukuwar hadurra irin wadannan.

''Su kansu masu jiragen ruwan za a tantance su domin ganin cewa jiragen nasu nada inganci, maimakon kyale abubuwa sasakai su ci gaba da faruwa'' inji shi.

Source: BBC