David Alaba ya koma Real Madrid daga Bayern Munich
Kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta cimma yarjejeniya da David Alaba domin ya murza mata leda tsawon kakar wasanni biyar.
Kungiyar bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Juma'a.
A cewarta za a kaddamar da David Alaba a matayin sabon dan wasan Real Madrid bayan kammala 2021 European Championship.
Dan wasan dan kasar Austria da ke tsaron baya ya je Bayern Munich ne a 2008.
Alaba, mai shekara 28, ya taimaka wa Bayern wajen daukar kofin Champions League a 2013 da 2020.