Yawancin fitattun mutane kan rike abin da suke yi da muhimmanci, amma wata 'yar wasan kwaikwayo a Indiya ta sadaukar da kanta da barin sana'arta domin taimaka wa manoma da ke zanga-zanga a kasar.
"Ina shirin daukar wani fim a wannan watan, amma yanzu sun cire ni daga fim din," in ji Sonia Mann a shirin BBC Outlook da ake yadawa ta radiyo.
Tun shekarar 2012 Sonia take sana'ar wasan kwaikwayo, kuma ta fito a fina-finai sama da 12 cikin harsunan Indiya daban-daban.
Fim din da ta fito a baya-bayan nan shi ne "Happy Hardy and Heer" - wanda aka dauki wani bangarensa a biranen London da Scotland - an kuma sake shi a shekarar da ta wuce. Mai yiwuwa shi ne fim dinta na karshe.
Abu ne mai wuya a fadi yadda ake kallon masana'antar Bollywood a Indiya. Amma Sonia ta juya wa "masana'antar fina-finai mafi girma a duniya" baya, wadda ke cike da tarin dukiya da daukaka, da fice fiye da tunanin dan adam.
Amma ta ce ba ta taba yin nadamar daukar matakin ba.
"Shiga zanga-zangar manoman ta sanya ni matukar farin ciki, da nutsuwa fiye da zama tauraruwar fina-finan Bollywood," in ji ta.
Kalubalantar gwamnatin Indiya abu ne mai matukar hatsari ga duk wani dan fim. A baya, taurarin fina-finai da ke sukar lamirin gwamnati na fuskantar turjiyar da kalubalen kin tace fina-finansu kafin fita kasuwa.
Sonia ta san shiga zanga-zangar manoman za ta shafi makomar sana'arta, an kuma gargade ta kada ta nunawa gwamnati yatsa.
Amma duk da haka ta ce ta ji ta gani.
Tsoro
Tun watan Satumbar bara, manoma daga jihohin Indiya daban-daban suka fara taruwa a wajen birnin Delhi domin yin zanga-zangar kin amincewa da matakin gwamnati na sauya doka kan yadda ake noma a kasar.
Firaiminista Narendra Modi da jam'iyyarsa ta BJP sun ce dokar za ta kara wa manoman kudaden shiga. Sai dai manoman sun ce sabanin hakan ne zai faru, tun da sauye-sauyen sun bai wa masu kamfanoni karfin iko.
"Na san cewa bashi ya yi wa yawancin manoman Indiya kanta. Ba sa samun isasshen tallafi daga gwamnati," in ji Sonia.
"Gwamnati ta ce mafi kankantar kudin da ake sayar da buhun masara mai nauyin kilogiram 100 zai kama rufi 1800, kwatankwacin dala 25 (Naira 12,250). Amma rufi 900 zuwa 1000 kadai manoma ke samu 1000."
"Magoya bayan gwamnati sun yi ta yawo da hotunan da nake sanye da dan kamfai a fina-finaina, tare da kalubalantar tarbiyyarta. Suna cewa ta yaya mace mara da'a za ta wakilci manoma. Sonia na kokarin dauke hankalinta daga kafafen sada zumunta, tana samun nutsuwa daga goyon bayan manoma.
"Tsofaffi na wa su ke kallona a matsayin 'yarsu. Ina ganin bacin rai a idanunsu. Sun amince da ni. Ba zan iya rabuwa da su ba..." in ji Sonia.
Zanga-zangar ta wuce ta ihu da kalaman batanci. Dubban manoma sun kafa sansani a kusa da babbar hanyar shiga birnin Delhi. Anan suke cin abinci, suke kwana. A ranar 1 ga watan Junairu aka tashi da tsananin sanyi.
"Yanayin ba mai kyau ba ne. Akwai tsauri sosai. Mutane da dama na tambayar me ya sa ba za ki koma otal ba? Na ce musu ba zan yi haka ba."
Tantuna
A yanzu kungiyoyin sa-kai sun samar da bandakuna. Sonia na shafe dare da rana da cin abinci a tantunan da aka kafa.
A yanzu kungiyoyin sa kai sun samar da bandakunan wanka da bahaya. Sonia na shafe dare da rana da cin abinci a tantunan da aka kafa.
Kamar sauran masu zanga-zangar, ita ma ta yi girki da wanke-wanke. Tana kuma taimakawa wajen rarrabawa masu zaman dirshan din abubuwan bukatu.
"Na sama wa mata 2,500 wajen kwana, ina ganin ya kamata mata suna bukatar wajen kwana. Na sama musu tantuna, da barguna da abinci. Yanzu da aka shigo bazara, na fara shirin sama musu fankoki."
Burinta ya rushe
Ta sanya kan ta tsundum cikin zanga-zangar, kuma tana fita ne kawai a lokutan da za yi wa magoya baya jawaban karfin gwiwa. Idan tana da lokaci ta kan yi magana a kan abin da ta rasa.
Sonia ta yi fim da shahararrun 'yan wasan Bollywood irinsu, Hrithik Roshan, da suke ba ta kwarin gwiwar sha'awar zama shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo.
"Mafarkina shi ne na fito a fim daya da Shahrukh Khan," in ji ta.
A yanzu ta san hakan ba za taba faruwa ba.
'Ni manomiya ce'
Sonia ta sanya an rufo mata wasikar a gilashi, ta makala a gidansu, bayan ta yi kwafin ta, kuma duk inda za ta je tana tare da ita.
"A duk lokacin da na karanta wasikar, sai na ji tamkar ina zaune kusa da shi, ina karanta abin da ke zuciyarsa."
Sonia ta ce a bayyane ta ke mahaifinta ya gyara karya zuwa gaskiya. A shekarar 2019 marubucin littafi kan rayuwar mahaifinta ya tambayi Sonia me ta rubuta game da mahifinta.
Ga abin da ta rubuta.
"Zuwa ga mahaifina, kai ne jagorana, abin alfaharina. Girmamawace kasancewarka mahaifina...ina fatan ka yi alfahari da ni, na kuma cika burinka da ka ke da su akai na, kamar yadda ka rubuta a wasikar da ka min."