Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Black Axe mafia: Ƴan sanda sun cafke ƴan Najeriya 30 da ke ayyukan asiri a Italiya

 118219750 3f21fbf5 9a86 40de Abba 61acd39a4f7f An cafke ƴan Najeriya 30 da ake zargin suna yi wa kungiyar mafiya ta Black Axe aiki

Jeu., 29 Avril 2021 Source: BBC

Ƴan sandan Italiya sun cafke wasu ƴan Najeriya 30 da ake zargin suna yi wa kungiyar mafiya ta Black Axe aiki a wani samame da suka kai a faɗin ƙasar.

A cewar jami'an yanzu haka mutanen da aka cafke na fuskantar tuhume-tuhume kusan 100 da suka hada da harkar miyagun ƙwayoyi da fataucin mutan da karuwanci da damfara ta intanet.

Ana zargin ƴan kungiyar na amfani da kudin intanet na Bitcoin don aiwatar da hada-hadar kudi a boye ta shafukan intanet.

A shekarun 1970 aka kafa kungiyar ta Black Axe a Nijeriya inda suka rika aiwatar da fyade da kisa don tsafi.

Sun kuma kafa rasa mai ƙarfi a ƙasashen ketare .

"Akwai shaidar da ta nuna cewa mambobin suna da alaƙa kai tsaye da ƙungiyoyi masu aikata miyagun laifuka a Najeriya, suna yin amfani da kalmomi iri ɗaya, alamomi da kuma tsubuce-tsubucen", in ji 'yan sandan Italiya.

An yi kamen ne a wasu larduna 14 da ke faɗin ƙasar kuma ciki harda jagoran ƙungiyar na ƙasar Italiya wanda wani mutum ne mai shekara 35 da ke zama a L'Aquila, da ke yankin Abruzzo.

'Ƙungiyoyin asiri na cin karensu ba babbaka a jami'o'in Najeriya'

Su wane ne Black Axe?

Ƙungiya ce mai ƙarfi ta tsafi da ta samo asali daga Najeriya.

A shekarun 1970 aka kafata, kuma a baya ana kiranta da 'Neo Black Movement'. Waɗanda suka ƙirkireta sun ce manufarsu ita ce samawa bakar-fata 'ƴanci'.

Sai dai a Jami'o'i, wadanda ƙungiyoyi babu alamar wata manufa ta siyasa tattare da su, face ayyukan tsafi da kashe-kashe da lalata.

Sun taka rawa wajen bijiro da wasu ƙungiyoyin asirin da suka yi suna a jami'o'in Najeriya irinsu Vikings da Eiye da Buccaneers.

Ƙungiyoyin na da kafar da suke bi wajen musayar bayanai ko batutuwa, kuma suna samun damar mallakar makamai da kuma kalar suturar da ake gane su da shi.

Suna da tsarin shugabanci irin na ƙungiyoyin fafutika, suna amfani da zaurance da kuma alamomi da ke alamta babban makamin ƙungiyar da kuma alamarta.

Ana yi wa mambobi alƙawarin kariya daga abokan adawa, amma akasari ana shiga ne domin samun mulki da ɗaukaka.

Irin waɗannan ƙungiyoyi haramtattu ne a Najeriya kuma an kama mabobinsu da dama tare da gurfanar da su a gaban kotu. Amma duk da haka ba su saurara da ayyukansu ba a ɗakunan kwanan ɗalibai na jami'o'i, inda suke ci gaba da samun sabbin mambobi.

Source: BBC