Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Onnoghen ya yi magana a kan dalilin da yasa Buhari ya cire shi

 117640732 9439a7d4 Cd29 44dc 8baf 56319b208776 Tsohon alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen

Sat, 20 Mar 2021 Source: BBC

Tsohon alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen ya yi bayani a kan dalilin da yasa aka cire shi daga mukaminsa a shekarar 2019.

Tun farko ya yi wasu kalamai game da kalubalen da ya fuskanta a ranar da ya cika shekara 70 da haihuwa a watan Disambar bara, wanda a wannan ranar ce ya kamata a ce ya yi ritaya daga aiki.

Sai dai ya yi karin haske a kan matsalolin da ya fuskanta a bikin kaddamar da wani littafi na wani babban lauya da aka yi a ranar Juma'a a birnin Abuja, inda ya musanta wasu daga cikin zarge-zargen da aka rika yi masa wadanda su ne suka sa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dauki mataki a kansa.

Mista Onnoghen ya musanta zargin da aka yi ma sa cewa ya gana da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda shi ne babban abokin hammaya na Shugaba Buhari a zabukan shekarar 2019.

Ya kuma karyata zargin cewa ya rika sakin wadanda ake tuhuma da almundahana lokacin da yake rike da mukamin alkalin alkalan kasar.

"Gabanin matakin da aka dauka na dakatar da ni daga aiki, babu wani zargi a kaina. An rika rade-radin cewa na gana da Atiku Abubakar a Dubai."

"A yanzu haka da nake magana, ban taba ganawar keke da Atiku ba . Bayan wannan kuma an zarge ni da sakin wasu manyan mutane da suka aikata miyagun laifuka, yayin da tun daga shekarar 1978 na daina sauraron kara a matsayin alkalin kotun tarayya."

A ranar 25 ga watan Janairu na shekarar 2019 ne Shugaba Buhari ya dakatar da Onnoghen daga aiki bayan sammacin kotun ladabtar da ma'aikatan da ya nemi ya gurfana a gabanta a kan tuhumar da ake yi masa ta rashin bayyana kadarorinsa.

Source: BBC