Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Sudan ta yi wa kwamandan ƴan tawaye afuwa

Flag Sudan Mista Hilal ya kasance kusa da tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir

Fri, 12 Mar 2021 Source: BBC

Sudan ta saki wani shugaban mayaƙan sa kai mai karfin faɗa a ji wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya wa takunkumi kan zargin aikata munanan ayyuka a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.

Afuwar da aka yiwa Musa Hilal, shugaban rundunar Janjaweed, ta biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu a kai, a watan Oktoban da ya gabata tsakanin gwamnatin riƙon ƙwaryar Sudan da ƙungiyoyin ƴan tawayen Darfur.

Mista Hilal ya kasance kusa da tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir amma ya samu saɓani da shi kuma aka cafke shi a shekarar 2017.

Kimanin mutum 300,000 aka kashe sannan mutane miliyan 2 da rabi suka rasa matsugunansu a tsawon shekaru na rikici a Darfur, yawancinsu tsakanin Larabawan Janjaweed da al'ummomin Afirka.

Source: BBC