Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Kasuwar musayar yan kwallo: Makomar Adreas Pereira, Konate, Fernandes, Koulibaly, da Jakobs

 114684948 Pereira Getty Wani dan kan kwallon Manchester United

Ven., 5 Mars 2021 Source: BBC

Arsenal na kan gaba cikin kungiyoyin da ke yunkurin daukar dan wasan RB Leipzig Ibrahim Konate mai shekara 21. (Standard).

Konte na daga cikin 'yan wasa shida da Arsenal suke sanya a gaba, yayin da kungiyar ke fatan sayar da dan wasan gabanta dan kasar Faransa Alexandre Lacazette mai shekara 29. (Football.London)

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya kara nuna shawa'a kan ɗan Aston Villa mai shekara 25 Jack Grealish, sai dai ita kungiyar da ke jan ragamar gasar Premier ta fi damuwa ta dauki dan wasan tsakiya na matsawa gaba da kuma mai bi ta bangaren hagu. (Mirror)

Dan wasan tsakiya na Manchester United dan kasar Portugal Bruno Fernandes mai shekara 26, ya shirya tsaf domin tsawaita kwataraginsa wanda hakan zai sanya a ninka masa kudin da ya ke dauka a mako zuwa fan 200,000 a mako. (Sun)

Kungiyar Leicester City na daf da daukar dan wasan Celtic da Faransa Odsonne Edouard mai shekara 23 kan kudi fam miliyan 15, shi ne dai dan wasan da kocin kungiyar Brendan Rodgers ke fatan ganin ya maye gurbin dan wasan gaban Ingila Jamie Vardy. (Mail)

Dan wasan bayan Masar Ahmed Elmohamady mai shekara 33 zai bar Aston Villaa karshen kakar wasanni, biyo bayan kin sabunta kwanatarginsa da kungiyar ke yunkurin yi. (Football Insider)

Napoli ta rage burin da ta sanya kan faranshin dan wasanta na baya Kalidou Koulibaly daga yuro miliyan 45 zuwa miliyan 38.7, Bayern Munich ke kan gaba wajen neman dan wasan sannan na Senegal mai shekara 29 sannan Liverpool da Manchester United. (Il Mattino - in Italian)

Manchester United na neman mafita kan dan wasanta na tsakiya Adreas Pereira mai shekara 25, saboda Lazio ta ce ba za ta iya sayan dan wasan na Brazil ba. (Corriere Dello Sport - in Italian)

Source: BBC