Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Barcelona: Joan Laporta zai jagoranci kungiyar a karo na biyu

 117486812 Gettyimages 1231585162 Joan Laporta ya sake nasara a zaben shugaban kungiyar Barcelona

Tue, 9 Mar 2021 Source: BBC

Joan Laporta ya sake nasara a zaben shugaban kungiyar Barcelona ta Spaniya a karo na biyu.

Laporta, a lokacin yakin neman zabe ya sha alwashin ci gaba da rike Lionel Messi a kungiyar.

Ya samu nasara da kashi 54 cikin 100 a yayin da Victor Font ya zama na biyu sai kuma Toni Freixa na uku.

Dan shekaru 58, shi ne ya nada Pep Guardiola a matsayin kocin kungiyar a lokacin yana shugaba a shekarar 2003 zuwa 2010.

Laporta zai maye gurbin Josep Maria Bartomeu wanda ya yi murabus a watan Oktoban bara.

Shi ne mutumin da ya dauko manyan 'yan wasa kamar su Ronaldinho na Brazil da kuma dan kwallon Kamaru Samuel Eto'o.

A wa'adin mulkinsa na farko, Barcelona ta lashe gasar zakarun Turai sau biyu, da na La Liga sau hudu da kuma na Copa del Rey.

Source: BBC