Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Yadda wata mata 'yar Najeriya ta yi fama domin ta rike ɗanta a Italiya

 118155878 Palermo Marykate Stanworth 8 Hoton uwan da danta

Dim., 2 Mai 2021 Source: BBC

Cikin jerin wasikun da muke samu daga 'yan jaridar Nahiyar Afrika, a wannan karon Ismail Einashe ya ga yadda wata uwa 'yar Najeriya da aka yi safarar ta zuwa Italiya ta kusa rasa danta - wani mummunan yanayi da mafi yawan matan Afrika ke fuskanta a Italiya.

Cikin wani yammaci mai dumi a birnin Sicily na Italiya, wata mahaifiya 'yar asalin Najeriya na tsaye a taga tana kallon yaronta dan shekara biyu yana wasa.

Suna zaune ne a wani bangare na gidan da suke rayuwa da wasu iyalai 'yan Afrika a Palermo.

Matar na zaune kan wata kujera tana jin dadin kallon yadda danta ke wasa a rana, a gefe guda kuma kamshin miyar nama ne yake tashi ana yi mata girki irin na mutanen Najeriya.

Sai dai matar mai shekara 25 na cike da wani labari na bacin rai, ta ce ba a jima ba da aka so kwace mata dan nata, lokacin da hukumomin da ke lura da wuraren da ake ajiye 'yan ci-rani suka je inda suke rayuwa a baya.

Mery, za mu kirata amma ba shi ne sunanta na gaskiya ba, ta zauna a Sicily na tsawon shekara biyar tun bayan da aka yi safararta daga yankin da aka haifeta na Niger Delta.

Kamar dai mafiya daga cikin matan Najeriya, ta je ne da alkawarin za ta samu aiki mai kyau, amma karshe aka tilasta mata yin karuwanci a Palermo.

Ta ce mata da yawa irinta da suke karuwanci na rayuwa ne cikin fargabar kar a kwace musu yara a kai wa wasu. Mery ta kara da cewa akwai kawayenta biyu 'yan Najeriya da aka yi wa haka.

Dukansu na zaune ne a tantunan da mafi yawan matan da aka yi safararsu ke kare rayuwarsu.

'Ba kamar yadda ake raino a Italiya ba'

Kuma mafi yawa kungiyoyin ba da agaji ne ke tafiyar da su a madadin gwamnatin Italiya, kuma an kawo su ne da manufar taimaka wa iyayen da suka shiga damuwa domin su warke.

Amma babu wanda ya isa ya fada maka yaran 'yan cirani nawa aa kwace aka kai gidan raino ko kuma aka bai wa wasu suka raine su, babu wadannan bayanan a Italiya.

A watan Satumbar 2018, Mary ta haifi danta bayan shekarun da ta kwashe ta fama da mawuyaciyar rayuwa a Palermo.

Ta fara soyayya da wani dan Najeriya wanda yake sanya ta farin ciki ba dadewa sai ta yi ciki. Kamata ya yi wannan ya zama lokaci mai dadi a wurinta amma sai ta kare da haihuwa a tantin 'yan ci-rani.

Lokacin da ta je wurin tsoro ya kara kamata na gudun kar ta rasa yaronta.

Ma'aikata a wurin sun shaida mata cewa za ta aini yaron ne kamar yara ake rainon yara a Italiya.

Abin da ya tayar musu da hankali shi ne yadda ake rainon yara a Afrika, yadda ake goya su a baya, yadda ake ba su abinci a baki da dai sauransu.

Ta gaya musu cewa a Najeriya ba wani abu ba ne uwa ta rike danta har ya girma ta wannan hanyar.

Sun ja mata kunnen cewa in ba ta daina ba, to za su shaida wa hukukomi wanda hakan kan iya janyo ta yi asarar dan nata.

Gwagwarmaya kan ɗa

Mary ta ce a wurin da suke rayuwa ma'aikata ba sa taimaka mata domin ta bai wa danta kulawar da ta kamata.

A watan Satumabr 2019 sai abubuwa suka rikice.

Hukumomin ba sa jin dadin yadda take kula da yaron wanda hakan yakai su ga ce-ce-ku-ce kuma abu ya yi kamari.

Abubuwa suka tsananta hukumomin suka nemi fitar da ita da danta dan shekara guda abin da ya kai su ga doke-doke ke nan.

Ta ce ta roke su kada su rabata da yaronta, ta yi ihu tace "kafin ku tafi da shi ku tabbatar kun kashe ni."

Dan kuwa sai kuka yake yi. Daga baya dai aka mayar mata da shi.

Nan da nan ta fara neman yadda za a yi ta bar wannan sansani, da taimakon kungiyoyin dai ta samu damar barin wurin a Nuwambar 2019.

Amma gabanin nan sai da ta gamsar da hukumomi cewa ita da saurayinta za su kula da yaronsu.

Kotun Turai ta goyi bayan wata uwa 'yar Najeriya.

Idan muka koma sansanin, da ma'aikatan sun fuskanci uwa ba za ta iya rainon yaron ba kamar yadda ya kamata ko kuma sun fuskanci za a iya samun hadari. Sai su tilasta rainonshi ta hanyar da suke so.

Idan uwar da ta fito daga Afrika ta zama ta saba da tsarin yana zama mawuyacin abu ta iya kalubalantar zargin cewa ba za ta iya kula da yaronta ba.

Idan kuma aka raba uwar da danta saboda ana ganin ba za ta iya rainon shi ba, to da wahala ta kara jin duriyar yaron ko kuma ta samu labarin shi ko ta samu wata hanya da za ta iya ganin shi.

Amma watakila a iya dawo musu da yaransu hannu.

A watan Afrilu, kotun turai kan kare hakkin dan adam ta yanke hukunci cewa hukumomin Italiya na take hakkin uwaye mata 'yan Najeriya ta hanyar raba su da yaransu da hukumomin suka yi birnin Rome a 2017.

Yaranta biyu an rainesu a gidan wasu Ialiyawa biyu a wurare daban-daban kuma an hanata ganinsu.

Kotun ta zargi hukumomin da rashin mutunta cewa uwar na da wata hanyar ta daban da suke amfani da ita a Najeriya wajen rainon yaransu.

A karshe dai kotun ta yanke hukuncin a biya mahaifiyar wasu kudade.

A ga Mary ita kakarta ta yanke saka.

A watan Satumbar 2020, ta auri wannan saurayin nata cikin farin ciki da jin dadi a Palermo.

Tana samun gamsuwa ganin yadda take kallon danta a kusa da ita, kuma a yanzu tana kokarin sa shi makaranta.

Ba mamaki wannan hukuncin da kotu ta yanke zai samar da kyakkyawan fata ga iyayen da suke 'yan ci-rani da ke zama a irin sansanonin wadanda ake kwacewa 'ya'ya.

Source: BBC