Opinions

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Pays

Kafar Chelsea daya ta kai daf da karshe a Champions League

 117876420 Masonmount Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Mason Moun

Ven., 9 Avril 2021 Source: BBC

Chelsea ta huce haushi a kan FC Porto, inda ta doke ta 2-0 a wasan farko na daf da na kusa da na karshe a Champions League da suka kara ranar Laraba.

Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Mason Mount daga baya ta ci na biyu daf da za a tashi ta hannun Ben Chilwell.

Ranar Asabar West Brom ta ci Chelsea 5-2 a gasar Premier da hakan ya kawo karshen wasa 14 da Thomas Tuchel ya yi a kungiyar ba tare da an doke shi ba a dukkan fafatawa.

Haka kuma Chelsea ta ci karo da kalubale a ranar Lahadi, bayan da Antonio Rudiger da Kepa Arrizabalaga suka yi rigima sai da aka shiga tsakaninsu a lokacin atisaye.

Porto ta Chelsea sun buga karawar ta Champions League a Sevilla a filin da ake kira Ramon Sanchez Pizjuan a Spaniya.

Hakan ya biyo bayan dokar hana shiga kasa tsakanin Portugal da Burtaniya domin gudun yada cutar korona.

Ranar 13 ga watan Afirilu Chelsea za ta karbi bakuncin FC Porto a wasa na biyu a dai Sevilla a matakin gidan kungiyar Stamford Bridge.

Source: BBC