Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Arsenal ta sha da kyar a hannun Fulham a Emirates

 118102471 Arsenalfc Daf da za a tashi daga wasan ne Gunners ta farke ta hannun Edward Keddar Nketiah

Mon, 19 Apr 2021 Source: BBC

Arsenal ta tashi 1-1 da Fulham a wasan mako na 32 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Emirates.

Fulham ta ci kwallon ne ta hannun Josh Maja a zagaye na biyu a fafatawar, bayan hutu da suka yi.

Daf da za a tashi daga wasan ne Gunners ta farke ta hannun Edward Keddar Nketiah da hakan ya sa suka rabi maki a tsakaninsu.

Fulham ba ta taba cin Arsenal ba a gida a wasan Premier 30 da suka yi, inda Gunners ta yi nasara a wasa 24 da canjaras shida kenan.

Da wannan sakamakon Arsenal tana nan a matakinta na tara a kan teburin Premier da maki 46.

Arsenal wadda za ta buga karawar daf da karshe da Villareal a Europa League, na fatan kara yin sama kafin a kammala wasannin bana.

Fulham tana ta ukun karshe a teburi da maki 27 da tazarar maki shida tsakaninta da Fulham ta 18.

Source: BBC