Menu

Ramadan: Abin da Musulunci ya ce kan azumin yara

 118229271 Gettyimages 538415256 594x594 Idan lokacin azumin ya zo, yara kan sha alwashin yin duka

Wed, 28 Apr 2021 Source: BBC

Akwai abubuwa da dama da yara ke ɗokinsu a duniya, kuma ana iya cewa azumin watan Ramadan na cikin na gaba-gaba musamman ga yaran da suka fara wayau.

Idan lokacin azumin ya zo, yara kan sha alwashin yin duka, ko kuma a ji a tsakaninsu suna fariyar wuce juna a yawan azumin da za su yi a wannan shekarar.

Har su kan tsokani wanda ba ya yin azumin ma a yi ta yi masa waƙar 'Gyande ba ya azumi'.

Haka kuma su ma iyaye, su kan ƙarfafa wa ƴaƴan nasu gwiwa wajen yi masu alƙawurra yi masu kyautar wani abu idan suka kai azumi.

Ga yaran da ba su yi ƙwari sosai ba ma, iyaye kan ƙarfafa masu gwiwar yin 'rabin azumi', wato daga lokacin sahur zuwa lokacin sallar Azahar - da haka har ka ji an ce "ai wance ta yi azumi ɗaya, amma da rabi-rabi".

Su kuma yaran a nasu ɓangaren su yi ta murna suna shelar cewa sun yi azumi.

To kamar ko wane ɓangare na addinin Musulunci, azumin watan Ramadan na da ƙa'idojinsa da hukunce-hukuncensa, misali mutanen da azumin ya wajaba a kansu da waɗanda za su iya ajiye wa da waɗanda dama can bai hau kansu ba.

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa yara na daga jerin mutanen da yin azumin bai zama dole a kansu ba.

Ya ce "Azumi ya ƙunshi barin cin abinci da barin shan ruwa da duk wani abu da ya shafi kusantar iyali."

"Allah Ta'ala cikin rahamarSa ya ce ba kowa ne zai iya yi tsawon sa'o'i bai ci abinci ba bai sha ruwa ba, cikinsu akwai yara da tsofaffi da marasa lafiya cikin mutanen da aka yanke azumi bai hau kansu na," a cewarsa.

Sai dai ya ce cikin wannan rukuni na mutane, an rarraba su cikin wanda za su rama azumin da wanda za su ciyar da miskini akwai kuma wanda ba za su ciyar ba kuma ba za su rama ba.

Yara wanda shekarunsu ba su kai na balaga ba na cikin mutanen da idan suka sha azumi ba za su rama ba kuma ba za su ciyar ba.

"An ɗauke alƙalami a kan yaro," a cewar Sheikh Daurawa. "Ana koya masu azumi ne don su saba, amma ba wajabi ba ne a kansu ba."

Sau da yawa, akwai iyayen da ke tilasta wa yaransu yin azumi don wasu dalilai, misali ko don tsoron yaron ba zai tashi da son yin azumi ba ko kuma don rashin sanin rashin wajibcin azimin a kansu.

Wani lokaci kuma iyaye kan kira ƴaƴansu da ragwaye idan suka kasa kai azumin da suka ɗauka.

Malamai da dama sun amince wannan ba dai-dai ba ne kuma bai dace a riƙa matsa wa yara yin azumin ba tunda Allah da kanSa bai sa su a jerin mutanen da azumi ya zama dole a kansu ba.

Amma da zarar yaro ya kai shekarun balaga, azumi ya hau kansa kuma idan bai yi ba yana da laifi, kamar yadda Sheikh Daurawa ya bayyana.

Yana da kyau a riƙa ƙarfafa wa yara gwiwar yin azumi don su saba kuma don su san falalarsa.

Riyas Izzedeen wanda ya girma a Sri Lanka amma a yanzu yake zaune a Landan ya ce ya fara yin azumi ne lokacin da yake da shekara bakwai. Ya ce a lokacin yana ɗaukar azumi ne don abokansa da ƴan gidansu duk suna yi.

Sai dai ya ce ba duka azumin ake barinsa ya yi ba "Wani lokaci sau ɗaya a mako guda ake bari na yi. Kuma idan na ɗauka na ji ba zan iya kai wa, ana bari na in karya musamman ma idan ranar makaranta ce," a cewarsa.

Ya kuma ce azumi ba ya hana su wasanninsu da suka saba.

"Za mu wuni a waje muna wasa da guje-guje da tuƙa kekunanmu, wasanni dai irin na yara. Mu kan gaji sannan mu ji ƙishirwa kuma duk mu ƙosa a kira sallar Magariba, amma wannan ba zai hana mu ɗaukar azumi wanshekare ba."

Riyas ya ce zai yi alfahari da ƴarsa ƴar shekara bakwai a yanzu idan ta yi azumi.

Source: BBC