Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Lionel Messi: Ya lashe takalmin zinare a La Liga ta bana

 118655352 Messigoldenboot Lionel Messi, kyaftin din Barcelona

Tue, 25 May 2021 Source: BBC

Barcelona ta tsira da Copa del Rey a kakar 2020/21, bayan da Atletico Madrid ta dauki La Liga a karon farko tun bayan 2013/14.

Shi kuwa Lionel Messi shi ne ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke gaba a cin kwallaye a gasar ta Sifaniya ta kakar nan.

Messi ya zura kwallo 30 a raga a bana ya kuma karbi kyautar da ake kira ta Pichichi, kuma karo na biyar a jere yana bajintar karo na takwas jumulla a tarihi.

Takalmin zinare takwas da ya lashe a La Liga a tarihi:

  1. Kakar 2009/10 (kwallo 34)


  2. Kakar 2011/12 (kwallo 50)


  3. Kakar 2012/13 (kwallo 46)
  4. Kakar 2016/17 (kwalo 37)


  5. Kakar 2017/18 (kwallo 34)


  6. Kakar 2018/19 (kwallo 36)


  7. Kakar 2019/20 (kwallo 25)


  8. Kakar 2020/21 (kwallo 30)


Source: BBC