Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Jami'an tsaro sun murƙushe yunƙurin sace ɗaliban sakandare 307 a Kaduna

 117571636 Af9d6656 57c2 46a0 B6ce 92dcd3e39fad Daliban ne suka sanar da jami'an tsaro lokacin da ƴan bindigar suka shigo makarantar

Mon, 15 Mar 2021 Source: BBC

Gwamnatin Kaduna ta ce ƴan bindiga sun sake kai hari wata makarantar sakandaren Ikara inda suka yi yunƙurin sace ɗaliban makarantar.

Kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna SAmuel Aruwan wanda ya tabbatar da harin ya ce ƴan bindigar sun abka makarantar sakandaren Kimiya GSSS Ikara ne da tsakar daren Asabar zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Ya ce daliban ne suka sanar da jami'an tsaro lokacin da ƴan bindigar suka shigo makarantar.

"Nan take jami'an tsaron da suka hada da sojoji da ƴan sanda da ƴan sa-kai suka ruga makarantar tare da yin artabu da yan bindigar, suka kore su," in ji shi.

Ya ce,"an ceto dalibai 307 ba tare da sun samu wani rauni ba" a harin da sojoji da suka murƙushe.

Source: BBC