Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Martinez zai bar Bayern Munich bayan shekara tara

Javi Martinez Bayern Munich Javi Martinez

Mer., 5 Mai 2021 Source: BBC

Javi Martinez zai bar Bayern Munich a karshen kakar bana, bayan shekara tara da ya yi a kungiyar ta Jamus.

Bayern ta ce ta tattauna da dan kwallon tawagar Spaniya cewar ba za ta tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a kungiyar ba, kuma dan wasan ya amince da hakan.

Munich ta dauki mai tsaron bayan mai buga tsakiya, Martinez a 2012 kan kudi Yuro miliyan 10 daga Athletic Bilbao a matakin wanda ta saya mafi tsada a lokacin.

Mai shekara 33 yana cikin 'yan wasan Munich da suka lashe kofi a 2013 da kuma uku a 2020, ya ci kofi 23 jumulla a kungiyar mai buga Bundesliga.

Bayern ta sanar cewar za ta karrama Martinez da David Alaba da Jerome Boateng da koci Hansi Flick - wadan da za su bar kungiyar a karshen kakar bana.

Source: BBC