Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Kungiyoyin farar hula na son gwamnatin Nijar ta kori ministan tsaro

 91539634 755916cd Db40 4fc3 8507 6c9e1029529f Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Sat, 20 Mar 2021 Source: BBC

Kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin 'yan adam na yankin jihar Tillaberi a Jamhuriyar Nijar sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta sallami ministan tsaro da na cikin gida game da gazawarsu wajen kare 'yan kasa daga hare-haren ta'addanci.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne cikin wata sanarwa da su ka fitar ranar Juma'a.

Lamarin kashe-kashe dai ya zama ruwan dare a yankin Tillaberi mai iyaka da Mali da kuma kasar Burkina-Faso, inda 'yan bindiga ke halaka jama'ar da ba su ji, ba su gani ba.

Ko a farkon makon nan, mutum sama da 50 aka kashe bayan sun fito daga cin kasuwa.

Cikin sanarwar, kungiyoyin sun yi bayanin yadda lamarin tsaro ya kasance a kasar da kuma yadda lamarin tsaro ke gudana a cikin jahar ta Tilaberi.

Kungiyoyin dai sun yi kira da Ministocin tsaro da na cikin gida na kasar ta Njar da su yi murabus.

Alzouma Moukaila Inero, mataimakin hadakar kungiyoyin farar hular masu zaman kansu na jahar Tilaberi ya bukaci a sauke ministocin a bai wa wadanda za su iya tafiyar da aikin samar da tsaron yadda ya kamata a yankinsu.

"Ba yadda za ta yi cewa kai ne kake tsaron kasa kuma ana kashe mutane, dukkan ministan da aka kashe mutane ba a bi wadanda suka kashe mutanen ba, kamata ya sauka, aikinsa bai yi ba". in ji Alzouma Moukaila Inero.

Hadakar kungiyoyin kare hakkin dan adam na yankin Tillaberi sun sanar da cewa sun damu ainun game da irin hare-haren kisan gilla da ake kai wa al'ummar fararen hula a jahar ta Tillaberi ba dare ba rana.

A baya-bayan nan ƴan bindiga suka kai wasu jerin hare-hare a yankin Banibangou na jahar ta Tillabery lamarin da ya yi sanadin aƙalla rayukan mutum 58 kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta ambato.

Maharan dai sun kai hare-haren ne kan motocin fasinja a harin da ake gani shi ne mafi muni da aka taba kaiwa.

Source: BBC